Isra'ila: Iran Ta Turje, Ta Yi Fatali da Zama a Teburin Tattauna wa da Amurka
- Iran ta ce ba za ta zauna tattaunawa da kowace ƙasa ba har sai Isra’ila ta dakatar da hare-haren da ta fara kai mata kwanaki takwas da suka gabata
- Ministan Harkokin Waje, Abbas Araghchi ya bayyana haka a lokacin da ake sa ran zai gana da takwarorinsa na Jamus, Faransa da Birtaniya a Geneva
- Iran, ta yi zargi cewa Donald Trump da nuna goyon baya ga Isra’ila, yayin da rahotanni ke nuna cewa sojojin Amurka na shirin kai hari kan Iran
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Kasar Iran –Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya bayyana cewa Tehran ba za ta zauna tattaunawa da kowace ƙasa ko ƙungiya ba har sai Isra’ila ta dakatar da hare-harenta.
Ana sa ran Araghchi zai gana da Ministocin harkokin wajen Jamus, Faransa da Birtaniya a birnin Geneva domin tattauna hanyoyin sassauta rikicin da ke ƙara tsananta tsakanin Iran da Isra’ila.

Kara karanta wannan
Kasashen Turai na fafutukar cimma tsagaita wuta yayin da Iran ta jefa makamai Isra'ila

Source: Twitter
Jaridar Arab News ta ruwaito cewa Araghchi ya ce gwamnatin Amurka na ƙoƙarin komawa teburin tattaunawa don duba batun shirye-shiryen nukiliyar Iran.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai ya ce Iran ta yi watsi da wannan tayin daga Amurka ganin yadda ta ke mara wa Isra'ila baya a harin ta'addancin da ta ke kai mata.
Kasar Amurka ta yi wa Iran tayin sulhu
Jaridar Israel Times ta kara da cewa gwamnatin Amurka ta aika da saƙonni da dama tana neman a zauna tattaunawa da Iran da gaggawa.
Araghchi ya ƙara da cewa:
“Mun bayyana cewa muddin hare-haren ba su tsaya ba, to babu wani gurbi na diflomasiyya ko tattaunawa.”
“Ba za mu zauna da Amurka ba sai Isra’ila ta dakatar da hare-haren da take kai mana.”
Iran: “Amurka na goyon bayan Isra’ila”
Ministan harkokin wajen Iran ya zargi gwamnatin Amurka, ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa Donald Trump, da nuna goyon baya ga Isra’ila a wannan yakin da ake gwabza wa.
Ya bayyana haka ne kwanaki kaɗan bayan da Trump ya ce yana duba yiwuwar shiga yakin kai tsaye ko kuma a ɗauki wani matakin daban.

Source: Twitter
Haka kuma wasu rahotanni sun bayyana cewa tuni sojojin Amurka suka fara shirye-shiryen kai hari kan Iran, inda ake zargin cewa harin na iya faruwa a ƙarshen makon da muke shirin shiga.
Sai dai duk da haka, Fadar White House ta fitar da sanarwa inda ta bayyana matsayinta na goyon bayan Isra’ila a cikin wannan rikici.
Amurka ta magantu kan harin Iran da Isra'ila
A baya, mun kawo labarin cewa Amurka ta ce Shugaba Donald Trump zai yanke shawarar ko Amurka za ta shiga yakin da ke gudana tsakanin Iran da Isra’ila cikin makonni biyu masu zuwa.
Ana ganin Trump na iya amfani da wa’adin makonni biyu don boye ainihin shirin sa na siyasa, musamman duba da yadda rikicin ke ƙara tsananta a yankin Gabas ta Tsakiya.
Wannan na faruwa ne a daidai lokacin da ƙasashen Iran da Isra’ila ke ci gaba da kai wa juna farmaki, abin da ke haifar da asarar rayuka da lalata dukiyoyi a yakin da Yahudawa suka jawo.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
