Wata Sabuwa: Makamai 2 da Ake Zargin An Harba a Yaƙin Iran da Isra'ila Sun Kauce Hanya

Wata Sabuwa: Makamai 2 da Ake Zargin An Harba a Yaƙin Iran da Isra'ila Sun Kauce Hanya

  • Wasu jirage marasa matuƙa da ake amfani da su a matsayin makami a yaƙin Iran da Isra'ila sun faɗa a yankin ƙasar Jordan
  • Hukumomin Jordan sun tabbatar da faruwar lamarin, inda suka ce yarinya yar shekara 12 ta samu rauni kuma an yi asarar dukiya
  • Tun farkon fara musayar wuta tsakanin Iran da Isra'ila, ƙasar Jordan ta rufe sararin samananta don gudun irin haka

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jordan - Jami’an Tsaro na Ƙasar Jordan (PSD) sun tabbatar da cewa makamai biyu da ake zargin suna da alaka da faɗan Iran da Isra'ila sun faɗo a ƙasarta kuma sun yi ɓarna.

Dakarun PSD sun bayyana cewa jirage marasa matuƙa da ake harbawa a matsayi makami sun faɗo a Jordan kuma sun jikkata wata yarinta da lalata dukiya.

Kara karanta wannan

Iran ta kai zazzafan farmaki kan tashar jirgin ƙasa, cibiyar fasaha da sansanin soji a Isra'ila

Ana zargin makamai 2 sun faɗa Jordan.
An samu matsala a musayar wuta tsakanin Iran da Isra'ila Hoto: Getty Image
Source: Getty Images

A cewarsu, makami ɗaya ya jikkata wata yarinya ‘yar shekara 12 a gundumar Azraq da ke gabashin ƙasar Jordan, ɗaya kuma ya jawo asarar dukiya a Ammān ta Arewa, in ji jaridar The New Arab

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jirage 2 sun kauce sun faɗa Jordan

A sanarwar da PSD ta fitar, lamarin na farko ya faru da sassafe a ranar Alhamis, ɗaya daga cikin jirage mara matuƙa ya faɗo a unguwar kasuwanci da ke Ammān ta Arewa, inda ya lalata wata motar farar hula da rufin tashar mota.

Sai dai rundunar tsaron PSD ta tabbatar da cewa babu wanda ya rasa ransa ko ya ji rauni sakamakon faɗuwar wannan makamai.

"Daga baya kuma, wani jirgi mara matuƙi ya faɗo a gundumar Azraq, inda ya jikkata yarinya ‘yar shekara 12, sannan ya lalata gidaje uku da motoci biyu," in ji PSD.

Wane mataki hukumomin Jordan suka ɗauka?

An bayyana cewa hukumomin tsaro da soji a ƙasar Jordan sun fara bincike kan duka haduran biyu, kamar yadda Premium Times ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kasar Iran ta canza ra'ayi game da tayin Trump, ta yi maganar yiwuwar sulhu da Isra'ila

Faɗowar waɗannan jirage na zuwa ne bayan rahotannin da PSD ta samu tun ranar Juma’a, cewa ana ganin wasu abubuwa na faɗowa. daga sama.

Ana zargin cewa abubuwan suna da alaƙa da makamai masu linzami da ake harbawa a yakin da ya ɓarke tsakanin Iran da Isra'ila.

A ranar Asabar da ta gabata, rahotanni sun ce mutane biyar sun jikkata bayan wani irin abu ya faɗo a kan wani gida a garin Irbid da ke arewacin Jordan.

Iran da Isra'ila na ci gaba da musayar wuta.
Hukumomin Jordan sun kaddamar da bincike kan faɗowar jiragen yaƙi marasa matuƙa Hoto: Getty Image
Source: Getty Images

Yaƙin Iran da Isra'ila ya fara shafar wasu

Wadannan lamurra na faruwa ne a daidai lokacin da tashin hankali ke ƙaruwa a yankin, bayan da Isra’ila ta kaddamar da munanan hare-haren sama kan Iran tun daga ranar Juma’a.

Saboda wannan rikici, Jordan ta rufe sararin samaniyarta sau da dama, ta kuma harba wasu abubuwa da suka kutsa cikin yankinta, tana jaddada cewa ba za ta zama filin yaƙi ga kowace ƙasa ba.

A ƙarshe, PSD ta gargaɗi jama’a da su guji kusantar guntun-guntun abubuwan da suka fāɗo daga sama, tana mai cewa suna iya zama masu haɗari.

Kara karanta wannan

Sanatocin Arewa sun yi matsaya kan matsalae rashin tsaro, an ba gwamnati shawara

Iran ta kai hare-hare zagaye na 15

A wani labarin, kun ji cewa dakarun juyin juya hali na ƙasar Iran wato IRGC sun sanar da kaddamar da wani sabon zagaye na hare-hare kan Isra'ila.

Dakarun sojin Iran sun ce wannan shi ne zagaye na 15 a jerin hare-haren da suke kai wa Isra'ila tun bayan ɓarkewar rikici tsaknin ƙasashen biyu.

IRGC ta kara da cewa tana ci gaba da amfani da jirage marasa matuƙa da masu yaƙi da kansu kuma su fashe wajen kai farmaki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262