Iran da Isra'ila: Khamenei Ya Yi Kalaman Nuna Tirjiya, Ya Karanto Ayar Kur'ani
- Jagoran juyin juya hali na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya bayyana cewa ƙasarsa za ta ci gaba da fuskantar Isra’ila ba tare da tsoro ba
- Khamenei ya ce shiga da Amurka ke yi cikin lamarin wata alama ce ta rauni da karancin ƙarfin Isra’ila
- Yayin da harin makamai tsakanin Iran da Isra’ila ke ci gaba, Khamenei ya ce nasara za ta kasance a ɓangaren gaskiya, bisa yardar Allah
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Iran - Jagoran juyin juya hali na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya fito fili da sababbin kalamai da suka nuna ƙarfin gwiwa da shirin ci gaba da tinkarar Isra’ila.
Ayatollah Ali Khamenei ya yi bayanin ne a lokacin da rikici ke kara tsananta tsakanin ƙasar Iran da Isra'ila.

Source: Getty Images
Legit Hausa ta tattaro bayanan da Ayatollah Ali Khamenei ya yi ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X.

Kara karanta wannan
Kasashen Turai na fafutukar cimma tsagaita wuta yayin da Iran ta jefa makamai Isra'ila
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tun makon da ya gabata, Iran da Isra’ila na ci gaba da musayar hare-haren makamai, lamarin da ke kara tayar da hankali a Gabas ta Tsakiya.
A cikin wannan hali ne Khamenei ya yi jawabi da ke ƙarfafa al’ummarsa da nuna rashin tsoron abokan gaba.
A lokaci guda, Amurka na nuna sha’awar shiga cikin rikicin don mara wa Isra’ila baya, sai dai shugaba Donald Trump ya ce zai yanke hukunci kan hakan cikin makonni biyu masu zuwa.
“Kada ku ji tsoro, ku jajirce” — Khamenei
A cikin jawabin da ya gabatar, Khamenei ya jaddada cewa idan makiya suka fahimci cewa Iran na jin tsoro, za su ci gaba da nuna mata danniya.
Ya ce:
“Ina son in gaya wa ƙasarmu mai albarka cewa idan makiyi ya fahimci kuna tsoro, ba zai taɓa barinku ba. Ku ci gaba da irin wannan hali da kuka tirje a kai; ku ci gaba da hakan da ƙarfin zuciya”
Ya kara da cewa kalaman da abokan Isra’ila daga Amurka ke fitarwa wata alama ce ta raunin Isra’ila da ƙarancin ƙarfin da take da shi wajen kare kanta.
“Nasara daga Allah ce” — Ayatollah Khamenei
Jagoran na Iran ya ambaci wata aya daga cikin Alƙur’ani mai girma don ƙarfafa gwiwar al’ummar Iran da kuma nuna tabbacin samun nasara.
Ya rubuta ayar da Allah ya ce: “‘Kuma nasara daga Allah ce, Maɗaukaki, Mai hikima’ (Ali Imran: 126).

Source: Getty Images
Shugaban ya kara da cewa:
"Kuma tabbas, Allah zai bai wa al’ummar Iran nasara, zai bai wa gaskiya nasara, da kuma ɓangaren da ke da gaskiya — in sha Allah.”
Wannan furuci na nuna irin tsarin tunanin Iran ne na ɗora kansu a kan tafarkin imani da amincewa da cewa suna cikin gaskiya, shi ya sa za su ci gaba da tunkarar Isra’ila.
Rasha ta goyi bayan Iran kan Isra'ila
A wani rahoton, kun ji cewa kasar Rasha ta goyi bayan Iran a yakin da ake cigaba da fafatawa tsakanin Tehran da Tel Aviv.
Shugaban Rasha ya bayyana haka ne yayin da Amurka ke barazanar shigawa Isra'ila fada, inda ya ce hakan na da hadari sosai.
A daya bangaren shugaban China ya bukaci a zauna a teburin sulhu domin shawo kan matsalar maimakon nuna karfin soja.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
