Iran: Bayan kai Hare Hare Masu Zafi, Isra'ila Ta Sake Yin Barazana kan Khamenei
- Yaƙin da ake fafatawa tsakanin Isra'ila da Iran na ƙara ɗaukar zafi yayin da ke ta musayar wuta a tsaknin ƙasashen biyu
- Ministan tsaron Isra'ila ya yi barazanar cewa ƙasarsa na iya kashe jagoran juyin juya hali na Iran, Ayatollah Ali Khamenei
- Israel Katz ya bayyana cewa bai kamata Khamenei ya ci gaba da rayuwa ba saboda burin da yake da shi na rusa ƙasar Isra'ila
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Gabas ta Tsakiya - Ƙasar Isra’ila ta yi barazanar kashe jagoran juyin juya hali na Iran, Ayatollah Ali Khamenei.
Ministan tsaron Isra'ila, Israel Katz, ne ya yi wannan barazanar kan Ayatollah Ali Khamenei.

Source: Getty Images
Tashar Aljazeera ta rahoto cewa ministan ya yi barazanar ne a wani gargaɗi mai tsanani da ya yi ga Ayatollah Ali Khamenei.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Isra'ila ta yi wa Ayayollah Khamenei barazana
Ministan tsaron na Isra’ila ya zargi Ayatollah Khamenei da kasancewa mutum da ke da burin rusa Isra’ila ta hannun wakilansa.
"Mutum kamar (Khamenei) kullum burinsa shi ne ya lalata Isra’ila ta hanyar wakilansa. Wannan mutum, wanda ke da niyyar kai mana hari, bai kamata ya rayu ba."
"Wannan batu, wato daƙile wannan mutum, kawar da shi, wani bangare ne na wannan yaƙi. Yanzu mun fahimci rawar da yake takawa, domin tun da farko yana magana ne a fili game da rusa Isra’ila."
- Israel Katz
Wannan furuci ya nuna mataki mai tsanani da Isra’ila ke ɗauka game da Khamenei, inda take ganin kashe shi wani ɓangare ne na shirin ta na dakatar da ƙoƙarin da ake zarginsa da yi na rusa ƙasar ta hanyar wakilansa.
Waɗannan kalaman sun fito ne bayan wani harin da Iran ta kai a garin Beersheba wanda ya yi ɓarna a Soroka.
Isra’ila tana ƙara nuna alamun cewa sauya gwamnati a Iran na daga cikin burin ta a wannan yaƙi da ta ƙaddamar da shi kwanan nan kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Kara karanta wannan
Babu hutu: Kasar Iran ta kai hare hare zagaye na 15 kan manyan birane 2 a Isra'ila
Netanyahu ya taɓo batun kashe Khamenei
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya kai ziyara asibitin Soroka da ke Beersheba, wani makami mai linzami na Iran ya lalata.

Source: Getty Images
A yayin ziyarar, Netanyahu ya ce ba zai cire yiwuwar kai farmaki kan Jagoran Iran Ayatollah Khamenei ba.
“Babu wanda ya ke da kariya daga hakan. Dukkan zaɓuɓɓuka a bude suke."
"Abin da ya fi shine kada a ci gaba da tattaunawa da manema labarai a kan wannan batu."
- Benjamin Netanyahu
A baya, ministan tsaron Isra’ila ya bayyana a fili cewa kawar da Khamenei na ɗaya daga cikin manufofin yaƙin da ƙasarsa ke yi da Iran.
Rasha ta goyi bayan Iran kan yaƙi da Isra'ila
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙasashen Rasha da China sun cimma matsaya ɗaya kan rikicin da ke faruwa tsakanin Isra'ila da Iran.
China da Rasha sun soki Isra'ila kan yaƙin da ta ƙaddamar a kan ƙasar Iran, inda suka buƙace ta da ta dakatar da faɗa.
Hakazalika Rasha ta ja kunnen Amurka kan ka da ta kuskura ta shiga cikin yaƙin da ƙasashen biyu ke gwabzawa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
