Abin da Muka Sani Game da Makamai Masu Linzami da Iran Take Harba wa Isra'ila
- Iran ta harba daruruwan makamai masu linzami zuwa Isra'ila bayan hare-hare kan cibiyoyin nukiliyarta da kisan hafsoshinta
- Makamai masu linzami sun kasance kayan yaki masu tafiyar dogon zango, tsananin gudunsu yana sa su ratsa nahiyoyi a 'yan mintuna
- A wannan rahoton, Legit Hausa ta tattaro muhimman abubuwan da ya kamata ku sani game da makaman da Iran ke harba wa Isra'ila
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Iran - Bayan hare-hare kan sansanonin nikiliyarta da kisan manyan hafsoshin sojinta, Iran ta harba daruruwan makamai masu linzami zuwa Isra'ila.
Ko da yake Isra'ila ta tare yawancin makaman da aka harba mata, amma da yawa sun samu damar tsallake tsaron nata, inda suka yi barna mai yawa, ciki har da waɗanda suka fada a tsakiyar Tel Aviv da sauran yankuna.

Kara karanta wannan
Isra'ila: Iran ta umarci jama'a su daina amfani da whatsApp, ta fadi sharrin manhajar

Source: Getty Images
Rahoton Aljazeera ya nuna cewa ba a san ainihin yawan makamai masu linzami da Iran ta mallaka ba, amma an ce tana a sahun gaba na kasashe masu yawan makaman.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda makamai masu linzami ke aiki
A cikin wannan rahoto, an yi bayani dalla-dalla kan yadda makamai masu linzami ke aiki da kuma yadda ake amfani da su a rikicin da ake ciki tsakanin Iran da Isra'ila.
Makamai masu linzami kayan yaki ne masu tafiyar dogon zango, waɗanda aka ƙera don isar da bama-bamai na al'ada ko na nukiliya ta hanyar bin wata hanya mai lankwasa.
Ana harba su ta hanyar amfani da injinan roka masu ƙarfi, wanda ke sa waɗannan makamai su tashi sama zuwa sararin samaniya ko ma sama da hakan, cikin tsananin gudu.
Da zarar injinansu sun daina aiki, makamin yana bin wata hanya da aka riga aka tsara masa, sannan zai sake lulawa cikin sararin samaniya kafin ya faɗa kan abin harinsa.
Iyakar nisan da makamai masu linzami
Makamai masu linzami na iya yin tafiyar nisan kilomita sama da 10,000, har ma su iya ratsa nahiyoyi. An rarraba makamai masu linzami bisa ga nisan tafiyar su kamar haka:
- Makamai masu gajeren zango na fagen yaki (BRBM): Suna tafiyar kasa da kilomita 200.
- Makamai masu gajeren zango (SRBM): Suna tafiyar kasa da kilomita 1,000.
- Makamai masu matsakaicin zango/tsaka-tsaki (MRBM/IRBM): Suna tafiyar kilomita 1,000 zuwa 3,500.
- Makamai masu dogon zango (LRBM): Suna tafiyar kilomita 3,500 zuwa 5,500.
- Makamai masu dogon zango da suke ratsa nahiyoyi (ICBM): Suna tafiyar fiye da kilomita 5,500.
Karfin gudun makamai masu linzami
Makamai masu linzami suna tafiya da sauri sosai, wanda ke ba su damar ratsa dubban kilomitoci a cikin 'yan mintoci kaɗan.
Ana auna saurin da suke tafiya a ma'aunin Mach, wanda shine daidai da gudun sauti; misali, Mach 5 yana nufin sau biyar na saurin sauti.
Galibi makamai masu linzami da ke tafiyar gajeren zango, na da karfin gudun fiye da Mach 1, ko a ce suna cin kimanin kilomita 1,225 a kowacce awa, ko mil 761 a kowace awa.
Amma, galibin makamai masu linzami da ke tafiyar dogon zango, suna iya tafiya da saurin wuce sauti mai tsananin gaske, fiye da Mach 5, watau kilomita 6,125 a cikin awa daya.

Source: Getty Images
Tsawon lokacin isar makaman Iran zuwa Isra'ila
Nisan dake tsakanin Iran da Isra'ila ya kai kimanin kilomita 1,300 zuwa 1,500 (mil 800-930), in ji rahoton Yahoo.
Makamai masu linzami daga Iran da ke tafiya a gudun Mach 5 za su iya kaiwa Isra'ila a kimanin minti 12, ko da yake ainihin lokacin ya dogara da nau'in makamin da kuma wurin da aka harba shi.
Me yasa ake wahalar dakile harin makamai masu linzami?
Babban abin da ke sa makamai masu linzami su zama masu haɗarin gaske shine haɗuwar dogon zango, saurin gudu, da kuma yadda suke da wahalar kakkabowa.
Saurin tafiyar su da kuma fasahar isa ga abin harinsu yana ba da ƙarancin lokaci ga shigifar tsaron samaniya mayar da martani don kakkabo su.
Haka kuma, a lokacin da injinsu suka daina aiki, suka sake lulalawa cikin sararin samaniya, to suna sauka da sauri ne, wanda ke sa tare su ta zama abu mai wahala.
Wasu makamai masu linzami kuma suna amfani da hanyoyin yaudara ko wasu matakan da suka dace don yaudarar shigifar tsaron makamai masu linzami, wanda hakan ke sa su zama masu wahalar tarwatsawa.
Abin da zai iya faruwa a rikicin Iran da Isra'ila
A wani labarin, mun ruwaito cewa, daruruwan mutane sun mutu yayin da wasu daruruwan suka jikkata a rikicin da ya barke tsakanin Isra'ila da Iran.
Ko da yake Amurka na musanta hannu a harin da Isra’ila ta kai Tehran, amma Iran na zargin cewa sojojin Amurka sun ba da goyon baya a boye.
Masana na daga cikin cewa abubuwa biyar za su iya faruwa a wannan rikici, ciki har da yiwuwar Iran ta farmaki kasashen Gulf da ta dade tana zargi da taimaka wa abokan gabar ta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


