Iran da Isra'ila na Cigaba da Asarar Rayuka yayin da Musayar Wuta Yayi Kamari

Iran da Isra'ila na Cigaba da Asarar Rayuka yayin da Musayar Wuta Yayi Kamari

  • Ma’aikatar lafiyar Isra’ila ta sanar da cewa tun daga daren jiya, mutane 154 aka garzaya da su asibiti bayan hare-haren da Iran ta kai mata
  • A nata bangaren, ma’aikatar lafiyar Iran ta ce Isra’ila ta kai mata hare-haren jiragen sama kan yankuna daban-daban tun daga ranar Juma’a
  • Tsamin dangantaka a tsakanin kasashen biyu ya kara kamari ne bayan Isra'ila ta kai wa Iran harin bazata, ta kashe manyan dakarunta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kasar Iran – Yayin da yaki ke tsananta a tsakanin Iran da Isra’ila, sababbin rahotanni daga hukumomin lafiya na ƙasashen biyu sun bayyana adadin mutanen da rikicin ya rutsa da su.

Ma’aikatar lafiyar Isra’ila ta sanar da cewa mutane 154 aka kai asibitoci daban-daban tun daga daren jiya sakamakon hare-haren da Iran ta kai.

Kara karanta wannan

"Komai ya tsaya," Iran ta samu gagarumar nasara da ta harba rokoki kan matatar man Isra'ila

Mutane da dama sun mutu a Iran da Isra'ila
Harin Iran kan Isra'ila ya jikkata mutane da dama Hoto: Benjamin Netanyahu/Getty
Source: Facebook

BBC ta wallafa cewa daga cikin wadanda suka jikkata, mutane hudu na cikin matsakaicin hali, yayin da mutum 130 suka samu rauni mai dama-dama.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaki yana kamari tsakanin Iran da Isra'ila

CNN ta ruwaito cewa Ma'aikatar lafiyar Iran ta ce yanzu haka mutane 15 na ci gaba da samun kulawar jami'an lafiya a yayin da mutane 5 kuma suna karɓar kulawa ta musamman sakamakon fargaba.

Hare-hare na kara kamari a tsakanin Isra'la da Iran
Harin Isra'ila a Iran ya kashe sama da mutum 220 Hoto: Getty
Source: Getty Images

A nata bangaren, ma’aikatar lafiyar Iran ta fitar da sabon bayani da ke nuna cewa akalla mutane 224 sun mutu, yayin da fiye da 1,200 suka jikkata sakamakon hare-haren jiragen saman Isra’ila.

Rahoton ya nuna cewa hare-haren da Isra’ila ke kaiwa sun shafi wurare da dama a cikin Iran, lamarin da ya haifar da asarar rayuka da lalacewar kayayyaki.

Kasar Iran ta kashe Isra'ilawa 24

A bangaren Isra’ila, hukumomin tsaron ƙasar sun bayyana cewa hare-haren da Iran ta kai cikin kwanakin nan sun hallaka mutane 24.

Kara karanta wannan

China ta fito fili, ta fallasa rawar da Trump ya taka a rikicin Iran da Isra'ila

An bayyana cewa waɗannan hare-haren suna mayar da hankali a kan sansanonin soja da kuma cibiyoyin leƙen asiri.

Masana tsaro na duniya da dama sun nuna damuwa kan yadda wannan rikici ke barazanar rikidewa zuwa yaƙi mai fadi wanda zai iya shafar dukan yankin Gabas ta Tsakiya.

Majalisar Ɗinkin Duniya da ƙasashe irinsu Amurka da Rasha na ci gaba da kiran bangarorin biyu da su dakatar da farmaki tare da komawa teburin tattaunawa.

Amurka na son Iran, Isra'ila su tsagaita wuta

A wani labarin, kun ji cewa Shugaban ƙasar Faransa, Emmanuel Macron, ya yi kira ga kasashen Iran da Isra’ila da su gaggauta dakatar da hare-haren da suke kai wa juna dake jawo asarar rayuka.

A wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a taron shugabannin ƙasashe G7 da aka gudanar a Kananaskis, Alberta, Kanada, Macron ya ce Amurka na kokarin shawo kan kasashen biyu.

Kiran Macron na zuwa ne a daidai lokacin da kasashen duniya ke nuna fargaba cewa rikicin na Iran da Isra’ila na iya rikidewa zuwa yaƙin wanda zai shafi yankin Gabas ta Tsakiya gaba ɗaya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng