"Komai Ya Tsaya," Iran Ta Samu Gagarumar Nasara da Ta Harba Rokoki kan Matatar Man Isra'ila
- Ƙasar Iran ta samu gagarumar nasara a sababbin hare-haren da ta kai Isra'ila yayin da yaƙi tsakanin ƙasashen biyu ke kara ta'azzara
- Hukumomin Isra'ila sun tabbatar da rufe matatar mai ta Haifa sakamakon harin roka da Iran ta kai
- Wannan dai na zuwa ne bayan Isra'ila ta kai hare-hare Iran a makon jiya, lamarin da ya sa Iran ta mayar da martani mai zafi
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Israel - Hukumar da ke kula da matatar mai a Haifa ta ƙasar Isra’ila, ta sanar da dakatar da dukkan ayyukanta bayan wani harin roka da Iran ta kai.
Kamfanin Bazan Group, wanda ke kula da matatar, ya bayyana cewa harin ya tilasta musu rufe ayyuka gaba ɗaya, yayin da rikicin ke kara zafi tsakanin Isra’ila da Iran ƙasashen da suka dade suna takun-saka.

Source: Getty Images
Rahoton Aminiya ya ce bayanin kamfanin ya ce rokokin da Iran ta harba sun lalata tashar wutar lantarki da matatar ke amfani da ita wajen sarrafa man fetur.
Iran ta lalata matatar man Isra'ila
Hakan ya janyo tsaikon aiki da kuma lalacewar ma’aikata uku sakamakon harin da Iran ta kai matatar, kamar yadda hukumomin Isra’ila suka tabbatar.
Hare-haren ramuwar gayya na Iran sun biyo bayan farmakin da Isra’ila ta kai a Iran, ciki har da babban birni Tehran, wanda ya yi sanadin mutuwar fiye da mutane 220.
Rahotanni sun ce mafi yawan wadanda suka mutu mata ne da yara, tare da wasu manyan jami’an tsaro da masana nukiliya na Iran, rahoton DW.
Me yasa Isra'ila ta tsokani faɗar Iran?
Isra’ila ta ce tana kai hare-haren ne domin hana Iran mallakar makamin nukiliya, wanda take zargin ƙasar na dab da kammalawa cikin wannan shekara.
Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ce hallaka jagoran addinin Iran, Ayatullah Ali Khamenei, na iya kawo ƙarshen rikicin gaba ɗaya.
Iran kuwa ta mayar da martani da cewa Isra’ila za ta dandana kudarta kan abin da ta kira da hare-haren ragonci da ta nufi fararen hula, cibiyoyin soja da kuma tashoshin makamashin nukiliya.

Source: Getty Images
Iran ta lalata muhimman wurare a Isra'ila
Duk da haka, Iran ta ce ba ta da niyyar dakatar da shirinta na nukiliya wanda take cewa manufarsa ita ce samar da wutar lantarki da makamashin zaman lafiya.
Ramuwar gayyar da Iran ta kai ta taɓa cibiyoyin soja, tashar wutar lantarki da matatar mai a Isra’ila.
Haka kuma ta yi sanadin mutuwar mutane sama da 24 da kuma lalata gine-gine a sassa daban-daban, ciki har da birnin Kudus da Tel Aviv.
China ta soki Trump kan rikicin Isra'ila da Iran
A wani rahoton, kun ji cewa Kasar China ta zargi Shugaba Donald Trump na ƙasar Amurka da rura wutar rikicin da ke faruwa tsakanin Iran da Isra'ila.

Kara karanta wannan
"Akwai matsala": Halin da Musulmin Iran ke ciki bayan luguden wutar Isra'ila a Tehran
China ta yi wannan zargin ne bayan Shugaba Trump ya buƙaci duka mutanen da ke zaune a birnin Tehran na ƙasar Iran, su gaggauta ficewa nan take.
China ta kuma bukaci 'yan ƙasarta da su bar Isra'ila saboda ƙaruwar rikici, lalacewar ababen more rayuwa, da yawaitar asarar rayuka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

