Saudiyya Ta Goyi bayan Iran yayin Ta ke Bata Kashi da Kasar Isra'ila
- Masarautar kasar Saudiyya ta bayyana tirjiya da Allah wadai kan hare-haren da Isra’ila ta kai a ƙasar Iran a ranar Juma'a
- Gwamnatin Saudiyya ta bayyana cewa hare-haren sun keta dokokin kasa da kasa da kuma 'yancin kasashe a duniya
- Sarkin Saudi ya amince da shawarwarin Yarima mai jiran gado domin tallafawa alhazai 'yan Iran har zuwa dawowarsu gida lafiya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Saudi Arabia - Masarautar Saudiyya ta fito karara tana caccakar Isra’ila bisa hare-haren da ta kai a ƙasar Iran.
Hakan na zuwa ne bayan Isra'ila ta kai hari kan cibiyoyin nukiliya, masana'antun makaman roka da kuma manyan hafsoshin sojin ƙasar.

Source: Facebook
Saudiyya ta wallafa a X cewa za ta ba mahajjatan Iran mafaka har zuwa lokacin da za a shawo kan rikicin kasar da Isra'ila.

Kara karanta wannan
Hormuz: Bayan ruwan wuta a Isra'ila, Iran ta toshe hanyar kai mai kasashen duniya
Kasar Saudiyya ta ce matakin kai harin ya sabawa doka da ka’idojin kasa da kasa tare da haifar da barazana ga zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.
Matsayar Saudiyya kan yakin Iran da Isra'ila
A wata sanarwa da Ma'aikatar Harkokin Wajen Saudiyya ta fitar a X a ranar 13 ga Yuni, 2025, ta ce harin na nuna tauye ‘yancin mulki da tsaron ƙasar Iran.
A cewar sanarwar:
“Masarautar Saudiyya na nuna kiyayya da Allah wadai da hare-haren da Isra’ila ta kai kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran wacce ƙasa ce ‘yar’uwarmu a addini da yanki.
"Wannan abu ya sabawa doka da ƙa’idodin kasa da kasa kuma ya tauye ‘yancin Iran da tsaronta.”
Sanarwar ta ci gaba da cewa:
“Duk da cewa Masarautar Saudiyya na tir da waɗannan hare-hare rashin imani,
"Tana kuma jaddada cewa al’ummar duniya da kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya na da babban nauyi na dakile rikicin nan take.”
Saudiyya za ta kula da alhazan kasar Iran
A wani mataki na nuna zumunci, Sarki Salman ya amince da shawarar Yarima mai jiran gado, Mohammed bin Salman, domin tabbatar da walwala da kare lafiyar alhazai ‘yan Iran da ke ƙasar.
An umurci Ma’aikatar Hajj da Umrah ta Saudiyya da ta ba su dukkan taimakon da suke bukata har zuwa lokacin da za a iya dawo da su cikin aminci zuwa ƙasarsu.

Source: Twitter
Wannan matakin na Saudiyya ya nuna irin ƙoƙarinta na kare martaba da zaman lafiya a tsakanin ƙasashen musulmi duk da rikicin siyasa da ya ɓarke a tsakanin Iran da Isra’ila.
Hare-haren da Isra’ila ta kai sun janyo ƙarin rashin jituwa a tsakanin ƙasashen duniya, inda ƙasashen Turai da na Larabawa ke ci gaba da bayyana damuwa kan yuwuwar faɗaɗa rikicin.
Iran ta toshe hanyar ruwan Hormuz
A wani rahoton, kun ji cewa Iran ta toshe hanyar jirgin ruwa da ake bi wajen shigar da danyen mai zuwa kasashen duniya.
Bincike ya nuna cewa kaso mai tsoka na danyen man da ke fita daga Gabas ta Tsakiya yana bi ne ta hanyar ruwan Hormuz.
Tunda aka fara rikicin Iran da Isra'ila kasashe suka fara gargadin jiragen ruwansu daga bi ta gabar ruwan domin kaucewa barazana.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

