Hajj 2022: Saudi Arabia ta kayyade shekarun mahajjata, duk wanda ya wuce 65 bashi da rabo bana

Hajj 2022: Saudi Arabia ta kayyade shekarun mahajjata, duk wanda ya wuce 65 bashi da rabo bana

  • Ma'aikatar Hajji da Umara ta Saudi Arabiya ta dakatar da wadanda ke da shekaru 65 ko ya haura kafin karshen watan Afirilu daga aikin Hajjin wannan shekarar
  • Baya ga sanya dokar shekarun, Ma'aikatar ta kara da wajabtawa mahajjata kammala rigakafin cutar Korona kamar yadda ma'aikatar lafiyan Saudi ta saka doka
  • An amince da dokar ne bayan dubi da abubuwa da dama wanda ya shafi lafiyar mahajjatan da gwamnati ta bukata, za'a sanar da iya yawan mutanen da ko wacce kasa zata kawo

Saudi Arabia - A ranar Asabar, Ma'aikatar Hajji da Umara ta Saudi Arabiya ta sanar da makurar shekaru 65 ga mahajjatan da zasu yi aikin Hajjin wannan shekarar. Ma'aikatar ta dakatar da wadanda suka shigar da bukatar yin aikin Hajji da suka kai shekaru 65 kafin watan Afirilu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Amurka ta amince Buhari ya kashe $1bn domin shigo da wasu jiragen yaki

Sa dokar Hajjin za ta zama alkhairi ga wadanda basu kai shekaru 65 ba. Hukuncin zai shafi mahajjatan da suka wuce shekaru 65, da kuma wadanda suka shigar da bukatar su da dattawa, mata ko tare da iyayensu a matsayin Muharramansu.

Hajj 2022: Saudi Arabia ta kayyade shekarun mahajjata, duk wanda ya wuce 65 bashi da rabo bana
Hajj 2022: Saudi Arabia ta kayyade shekarun mahajjata, duk wanda ya wuce 65 bashi da rabo bana. Hoto daga theislamicinformation.com
Asali: UGC

Sai dai, an bayyana cewa wadanda suka shigar da bukatar aikin Hajjin kuma dokar shekarun ta shafesu, amma suka cike sauran sharuddan za su iya sake shigar da bukatar a yanar gizo kafin 22 ga watan Afirilu.

Baya ga sanya dokar shekarun, Ma'aikatar ta kara da wajabtawa mahajjata kammala rigakafin cutar Korona, kamar yadda ma'aikatar lafiyan Saudi ta amince, The Islamic Information ta ruwaito.

Bugu da kari, dole mahajjatan da zasu taso daga kasashen ketare su yi gwajen cutar Korona kuma a tabbatar basa dauke da cutar wanda bai wuce awanni 72 kafin tasowarsu zuwa Saudi Arabiya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya ta fara rabon buhunan abinci kamar yadda Buhari ya bada umarni

Ma'aikatar Hajji da Umara ta Saudi Arabiya ta kara da jaddada cewa, dole mahajjata su bi dokar Korona, gami da bin dokar yayin bauta.

Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Saudi ( SPA) ta ruwaito, sanya dokar tazo ne bayan dubi da abubuwa da dama, wadanda suka hada da tabbatar da lafiyar mahajjatan da gwamnati ta bukata don tabbatar da cigaba da aikin Hajji duk da yayin barkewar cutar Korona.

Ma’aikatar ta ce, za'a sanar da yawan mahajjatan da zasu amince da su nan ba da dadewa ba.

Fitaccen Malami a Saudiyya ya ce babu laifi yin bikin ranar zagayowar haihuwa a Musulunci

A wani labari na daban, Dr. Qais Bin Muhammad Al-Sheikh Mubarak, tsohon mamban kungiyar manyan malaman Saudi Arabiya, ya ce babu laifi idan musulmi ya yi murnar shagalin bikin al'ada irin su, murnar zagayowar haihuwarsa ko na masoyansa.

Jaridar Saudi Gazette ta ruwaito cewa, hakan bai da bambamci da murnar zagayowar ranar aure, samun karin girma ko matsayin mutum ko na 'ya'ya, samun damar kammala digiri ko kammala karatu daga jami'a, ko sauran bukukuwa, a cewarsa.

Kara karanta wannan

Ko Buhari ya sauka matsalar tsaro ba za ta kare ba, Fadar Buhari ga dattawan Arewa

Asali: Legit.ng

Online view pixel