Jerin Kasashe 10 a Afirka da Suka Fi Ko’ina Arhar Man Fetur a Watan Mayun 2025
Duk da ƙalubalen ƙarancin makamashi da sauye-sauye a harkar man fetur da gas, wasu ƙasashen Afirka sun shiga jerin ƙasashen da fetur ke da arha a duniya a watan Mayu, 2025.
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Libya ce ta fi kowace ƙasa a nahiyar samun fetur tare da sayar da shi da arha, inda Angola da Algeria suka zamo ƙasashen da ke binta a baya.

Source: UGC
Kasashen Afirka 10 mafi arhar fetur
Nijeriya na matsayi na 5 a Afirka da kuma na 12 a duniya kamar yadda rahoton jaridar The Guardian ya nuna.
Samun fetur a farashi mai rahusa a Afirka yana da matuƙar muhimmanci, musamman ga ƙasashen da ba su da nau'ikan makamashi masu yawa.
Masana'antun tace mai da suka ci gaba sun ba wasu ƙasashen damar samar da fetur mai araha kuma suna samun riba mai yawa.
Ga jerin ƙasashe 10 na Afirka da ake samun man fetur a farashi mafi araha a watan Mayun 2025 bisa ga bayanan GlobalPetrolPrices.com:
1. Libya
A Libya, ana sayar da lita ɗaya ta fetur a kan $0.027 (₦43.34). An ce albarkatun mai da tallafin gwamnati sun sa farashin fetur ya sauka ƙasa a ƙwarai.
Duk da rikice-rikicen siyasa, Libya na ci gaba da amfani da albarkatunta domin samar da makamashi mai arha ga jama’arta.
2. Angola
Farashin lita ɗaya a Angola ya kai $0.327 (₦522.67). A matsayinta na babbar mai fitar da mai a Afirka, Angola na cin gajiyar samar da fetur a cikin gida.
Sai dai gwamnati na fama da daidaito tsakanin tallafin mai da samun kudin shiga, musamman wajen kokarin fadada tattalin arziki na kasar.
3. Algeria
A Algeria, ana sayar da litar fetur a kan $0.346 (₦553.00). Ƙasar na ɗaya daga cikin manyan masu samar da mai da gas.
An ce Algeria na amfani da biyan tallafi don saukaka farashin makamashi ga jama’a. Sai dai a yanzu gwamnati na samun matsin lamba kan sake tsarin biyan tallafi domin daidaita kasafin kuɗin kasar.

Kara karanta wannan
Fursunoni 7 sun faki idon jami'ai, sun tsere daga gidan yari ana sheka ruwan sama
4. Masar (Egypt)
Masar na sayar da fetur a kan $0.381 (₦608.30) kan kowace lita. Duk da cewa an rage biyan kudin tallafi a wasu shekarun baya, sai dai har yanzu fetur na da arha a kasar.
Yayin da 'yan kasar ke samun mai da arha, an ce wannan matakin yana taimakawa wajen bunkasa tattalin arziki da walwalar al’umma.
5. Najeriya
A Najeriya, ana sayar da fetur a kan $0.532 (₦849.50) kan kowace lita, yayin da matatar Dangote ke sayar da shi kan N825, kamar yadda muka ruwaito.
Duk da kasancewar ita ce kasa mafi girma wajen fitar da man fetur a Afirka, ƙasar na fama da sauye-sauyen tsarin tallafi da karancin mai a wasu lokuta.
Farashin man fetur yakan canja a kowane lokaci, yayin da ya yi kololuwar tsada bayan gwamnatin kasar ta cire tallafin mai.

Source: Getty Images
6. Sudan
Litar farashin man fetur a Sudan ya kai $0.700 (₦1,118.33). Rikicin siyasa da matsin tattalin arziki sun shafi farashin mai a ƙasar.
Duk da cewa gwamnati na biyan tallafin mai, hakan bai hana ta fuskantar matsin lamba daga hauhawar farashi da faɗuwar darajar kuɗin ƙasar ba.
7. Tunisia
A Tunisia, ana sayar da fetur a kan $0.840 (₦1,341.99) kan kowace lita, inda ta ke matsayi na 28 a duniya.
Duk da cewa ƙasar na shigo da yawancin makamashinta daga waje, tallafin gwamnati na rage wa jama’a nauyin farashin.
Sai dai ana fargabar hauhawar bukatu da sauye-sauyen tattalin arziki zai shafi farashin man fetur din a nan gaba.
8. Liberia
Farashin fetur a Liberia ya kai $0.871 (₦1,391.73) kan kowace lita. Kasancewar ƙasar ta dogara da shigo da fetur ya sa farashi ya yi tsada, saboda biyan kuɗin jigila da tsadar shigo da kaya.
Kokarin gwamnati na daidaita tattalin arziki da inganta ababen more rayuwa na da muhimmanci wajen tabbatar da dorewar farashin.
9. Habasha (Ethiopia)
A Habasha, ana sayar da litar man fetur a kan $0.927 (₦1,480.20). Saboda ƙasar ba ta samar da fetur da kanta, farashin yana da nasaba da sauye-sauyen farashin fetur a kasuwannin duniya.
Gwamnatin Habasha na kokarin rage dogaro da shigo da kaya ta hanyar saka jari a masana’antu da hanyoyin sufuri.
10. Gabon
A Gabon, farashin lita ɗaya na fetur ya kai $1.020 (₦1,630.26). Duk da kasancewarta ƙasa mai fitar da fetur, ana samun ragin farashi saboda samar da shi da ake yi a cikin gida.
Sai dai kokarin ƙasar na rage dogaro da fetur yana ci gaba da kasancewa wani babban buri da ya har yanzu bai tabbatu ba.
Farashin fetur ya ki sauka duk da matakin Dangote
A wani labarin, mun ruwaito cewa, duk da cewa Dangote ya rage farashin man fetur zuwa tsakanin N875 da N905, gidajen mai sun ƙi canza farashin da suke sayarwa.
Matatar Dangote ta sauƙaƙe farashin sau shida a cikin 2025, amma har yanzu ana sayar da man fetur tsakanin N890 zuwa N910 a gidajen mai.
Masu gidajen mai sun koka game da rage farashin ba tare da sanarwa ba, suna masu cewa hakan yana haifar musu da asara da rage riba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


