'Yara Miliyan 1.5 Za Su Mutu': Najeriya na Fuskantar Sabuwar Barazana daga Trump

'Yara Miliyan 1.5 Za Su Mutu': Najeriya na Fuskantar Sabuwar Barazana daga Trump

  • Gwamnatin Amurka na shirin daina bai wa GAVI tallafi, wata kungiya da ke bayar da rigakafi a kasashe masu tasowa, ciki har da Najeriya
  • Rahoton USAID ya nuna cewa an soke yarjeniyoyi 5,341 na tallafi da darajarsu ta kai dala biliyan 76, ciki har da yaki da zazzabin masassara
  • Dakatar da tallafin Amurka ga GAVI na iya haddasa mutuwar yara miliyan 1.2 cikin shekaru biyar masu zuwa saboda rashin rigakafi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Amurka - Gwamnatin Amurka na shirin dakatar da bayar da tallafi ga GAVI, wata kungiya da ke samar da tallafin rigakafi ga kasashe masu tasowa, ciki har da Najeriya.

Wani rahoto da hukumar USAID ta fitar ya nuna cewa gwamnatin Shugaba Donald Trump tana shirin rage ayyukan yaki da cutar zazzabin cizon sauro.

Kara karanta wannan

IYC: Rikicin Ribas ya dawo sabo, kungiyar duniya ta kalubalanci shugaban riko

USAID ta fitar da rahoton da ke nuna shirin Amurka na dakatar da shirin GAVI da zai shafi Najeriya
Najeriya da wasu kasashe za su rasa tallafin rigakafin zazzabin cizon sauro saboda matakin Amurka. Hoto: @officialABAT, @Trump
Asali: Getty Images

Janyewar tallafi daga shirye-shiryen lafiya

A cewar kafar labaran Reuters, an mika rahoton da ke bayani kan shirye-shiryen tallafin kasa da kasa da za a soke ga ‘yan majalisar dokokin Amurka, a ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya nuna cewa za a soke jimillar yarjeniyoyi 5,341, wanda darajarsu ta kai kusan $76bn, yayin da Amurka ta riga ta ware kusan $48bn don aiwatar da wasu shirye-shirye.

An ce, wannan tallafin na $48bn da aka ware, zai ci gaba da taimaka wa ayyukan yaki da cutar kanjamau da tarin fuka, da kuma samar da agajin abinci ga kasashen da ke fama da yakin basasa da bala’o’i na dabi’a.

Duk da haka, Amurka za ta dakatar da mafi yawan shirye-shiryenta na lafiya, ciki har da yaki da cutar zazzabin cizon sauro, wadda ta yi kamari a Najeriya.

Tasirin dakatar da tallafin Amurka ga yara

A cewar mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka, an dakatar da shirye-shiryen da ba su dace da manufofin gwamnati ko muradun kasar ba.

Kara karanta wannan

Siyasar Rivers: Shugaban riko ya sauke dukkan mutanen da Fubara ya nada

Ya bayyana cewa:

"An tantance kowanne shiri don tabbatar da cewa yana cikin ajandar gwamnatin Amurka. Akwai muhimman shirye-shiryen USAID da za su ci gaba da gudana."

Sai dai, shugabar gudanar da shirin tallafi karkashin GAVI, Sania Nishtar, ta ce wannan matakin zai haddasa mutuwar miliyoyin yara.

Ta bayyana wa jaridar kasa da kasar cewa Amurka na bayar da tallafin shekara-shekara na dala miliyan 300 ga GAVI, wanda ke da muhimmanci ga ayyukanta.

A mako mai zuwa, Mrs. Nishtar tare da shugaban hukumar GAVI, José Barroso, za su je Washington don neman ci gaba da samun tallafin Amurka.

“Idan ba mu samu tallafin Amurka ba, hakan na nufin mutuwar yara miliyan 1.2 cikin shekaru biyar masu zuwa saboda rashin rigakafin cututtuka kamar cizon sauro da diphtheria,” inji Mrs. Nishtar.

Mrs. Nishtar ta kara da cewa: "Ina fatan tattaunawa kan lamarin. Muna fatan ba a yanke hukunci na karshe ba."

Kara karanta wannan

Masu bautar kasa a Najeriya na cikin alheri dumu dumu, Tinubu ya fara biyan N77, 000

Tasirin manufofin Trump kan kungiyoyin lafiya

Amurka ta yi sauye sauye ga kungiyoyin da ta ke ba tallafin ayyukan jin kai
Amurka: Yadda manufofin Shugaba Trump suke da tasiri ga kungiyoyin kiwon lafiya na kasa da kasa. Hoto: @realDonaldTrump
Asali: Twitter

GAVI na daga cikin kungiyoyin kiwon lafiya na duniya da za su fuskanci matsin lamba sakamakon manufar gwamnatin Donald Trump ta "Amurka Farko".

Tun bayan komawarsa Fadar White House, gwamnatinsa ta rage tallafi ga Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da kuma soke sama da kashi 80% na kwangilolinta.

A watan Janairu, Shugaba Trump ya dakatar da tallafin WHO da duk wani agajin da ake bayarwa ga kasashe masu tasowa, matakin da ya yi matukar shafar harkokin lafiya a Najeriya.

Illar dakatar da ayyukan USAID ga Bauchi

A wani labarin, mun ruwaito cewa, dakatar da ayyukan USAID bisa umarnin Shugaban Amurka, Donald Trump, ya shafi shirin ba da tazarar haihuwa a jihar Bauchi,

Shugaban hukumar kula da lafiya a matakin farko a Bauchi, Dakta Rilwanu Mohammed, ya ce rashin tallafin ya hana rarraba kayan tsara iyali ga masu bukata a jihar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng