Zargin Lalata: Sanata Natasha Ta Tafi Birtaniya, Ta Sake Tono Wani 'Sirrin' Akpabio

Zargin Lalata: Sanata Natasha Ta Tafi Birtaniya, Ta Sake Tono Wani 'Sirrin' Akpabio

  • Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta ce an dakatar da ita daga majalisa bayan ta shigar da korafi kan cin zarafi da Godswill Akpabio ya yi mata
  • A cewarta, Akpabio yana matsa mata lamba cewa dole ne ta "biya masa bukata" idan ta na son samun damarmakin ofisinta a majalisar dattawa
  • Yayin da ta nemi a janye dakatarwar da aka yi mata, Natasha ta ce ta shafe sama da shekara tana jure yunkurin cin zarafi daga Akpabio

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Birtaniya - Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta ce dakatarwar da aka yi mata na tsawon watanni shida na da nasaba da korafin da ta shigar kan Sanata Godswill Akpabio.

A wata hira da ta yi da babban talabijin na Birtaniya, sanatar ta ce ta kwashe fiye da shekara guda tana fama da yunkurin cin zarafi daga shugaban majalisar dattawa.

Kara karanta wannan

Akpabio: Kotu ta girgiza Natasha, alkali ya sauya hukunci kan dakatar da ita a majalisa

Natasha ta yi magana a Birtaniya kan yadda Akpabio ya rika nemanta da lalata
Sanata Natasha ta budewa duniya yadda Akpabio ya shafe shekara yana nemanta da lalata. Hoto: @NGRSenate
Asali: Twitter

'Yar majalisar ta shaidawa Sky News cewa Akpabio yana matsa mata lamba a koyaushe, yana cewa dole ne ta "biya masa bukata" idan har tana son samun damarmakin ofisinta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Dalilin dakatar da ni daga majalisa' - Natasha

A cewar Sanata Natasha, ta shigar da korafi a ranar 5 ga Maris, 2025, amma abin mamaki washegari aka dakatar da ita daga majalisar dattawa.

"Na shigar da karar cin zarafin da aka yi min, amma sai aka dakatar da ni washegari, wanda hakan ya nuna an yi ne don a toshe min baki," inji Natasha.

Ta bayyana dakatarwar a matsayin haramtacciya da aka yi bisa zalunci, tana mai cewa hakan hanya ce ta hana ta yin magana kan abin da ya faru da ita.

A yayin hirar, an tunatar da ita cewa majalisar dattawa ta ce an dakatar da ita bisa zargin aikata "laifi mai tsanani," sai dai ta ce hakan ba gaskiya ba ne.

Kara karanta wannan

Zargin lalata: Sanata Natasha ta kasa hakura, ta sake sabuwar fallasa kan Akpabio

Sanata Natasha ta ce:

"Sun ce an dakatar da ni saboda laifi mai tsanani, to amma menene laifin da na aikata da ya kai a dakatar da ni har na watanni shida?"

Ta ce ba ta aikata wani laifi ba, illa dai ta ki amincewa da matsin lamba daga shugaban majalisa, wanda hakan ne ya janyo mata matsala.

"An fi ba maza kariya a majalisa" - Sanata Natasha

Sanatar mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, ta bayyana cewa ta sha ganin mazaje a majalisa suna fada da juna, suna jifan kansu da abubuwa, amma ba a taba dakatar da su ba.

"Na sha ganin ‘yan majalisa maza suna fada, suna yi wa juna ihu da zagi, amma ba a taba dakatar da su ba. Me ya sa?," Natasha ta tambaya.

Ta ce an dauki mataki a kanta kawai don ita mace ce, wanda hakan ya nuna rashin adalci da nuna bambanci a majalisar.

Kara karanta wannan

"Majalisa ta koma kamar kungiyar asiri," Natasha ta fadi abin da Sanatoci ke tsoro

Sanatar ta ce Akpabio ya sha gaya mata cewa idan har tana son cin moriyar ofisinta, dole ne ta "biya masa bukatarsa don ya ji dadi."

A cewarta:

"Ya na yawan ce mun, 'Ni ne babba a nan, dole ki faranta min rai idan har ki na son ki sami damarmakin da sauran ‘yan majalisa ke samu.'"

Sanatar ta nemi Akpabio ya janye dakatarwar

'Yar majisar dattawan ta ce saboda kin amincewarta da bukatar Akpabio, hakan ya haifar da gaba da kuma yunkurin dakile hakkokinta a majalisar.

A karshe, Sanatar Natasha Akpoti-Uduaghan ta bukaci a janye dakatarwar da aka yi mata tare da gudanar da bincike kan cin zarafin da take zargi.

Ta ce dakatarwar da aka yi mata ba bisa ka’ida ba ne, kuma hanya ce ta hana ta yin magana kan abin da ya shafe ta.

Har zuwa yanzu, shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, bai yi martani kan wadannan zarge-zarge da sanatar ke yi masa ba.

Kara karanta wannan

Majalisa ta dauki matakin farko na tsige gwamna Fubara, ta jero tuhume tuhume

Kalli hirar da aka yi da Natasha a nan kasa:

'Abin da ya faru a daren auren Natasha' - Akpabio

A wani labarin, mun ruwaito cewa, shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya ce ya na da kyakkyawar alaka da mijin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, Emmanuel Uduaghan.

Akpabio ya ce Uduaghan abokinsa ne, domin har ya halarci bikin aurensa, inda ya kwana a masana’antar simintin Dangote da ke Obajana, a daren auren Natasha.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng