Matar da Ta fi Kowa Tsufa a Duniya Ta Mutu Tana da Shekaru 117, Bayanai Sun Fito

Matar da Ta fi Kowa Tsufa a Duniya Ta Mutu Tana da Shekaru 117, Bayanai Sun Fito

  • Matar da ta fi kowa tsufa a duniya, 'yar kasar Spain, Mariya Branyas Morera ta mutu tana da shekaru 117 a duniya, a cewar iyalanta
  • An ce Mariya Branyas ta tsallake yakin duniya na 1936-39 da kuma annobar murar tsuntsaye ta Spain a 1918 da COVID-19 a 2020-2021
  • Hukumar ba da kambu ta duniya ta nada Mariya Branyas a matsayin wadda ta fi kowa tsufa a duniya, bayan mutuwar Lucile Randon

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Spain - Maria Branyas, wanda ta kasance macen da ta fi kowa tsufa a duniya ta mutu a wani gidan kula da tsofaffi da ke Spain tana da shekaru 117.

An ruwaito cewa Mariya Branyas ta mutu ne a ranar Talata bayan ta wallafa wani dan karamin sako a shafinta na sada zumunta a ranar.

Kara karanta wannan

Murna za ta koma ciki? Ambaliya ta fara barazana ga wadatar abinci

Maria Branyas, wadda ta fi kowa tsufa a duniya ta rigamu gidan gaskiya
An sanar da mutuwar Maria Branyas, wadda ta fi kowa tsufa a duniya. Hoto: @MariaBranyas112
Asali: Twitter

Wanda da ta fi kowa tsufa ta mutu

An fitar da labarin mutuwar Maria ne a shafinta na X, inda ta ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Maria Branyas ta tafi ta barmu. Ta mutu kamar yadda ta bukata: a cikin barcinta, cikin kwanciyar hankali kuma babu ciwo."

Wani ma'aici a gidan kula da dattawan ya tabbatar da mutuwar tsohuwar, duk da cewa bai yi karin haske a kan lamarin ba.

Maria ta yi nuni da cewa ba makawa mutuwarta ta kusanto ta a ranar Litinin, kamar yadda ta wallafa a shafinta tana mai cewa:

"Ina jikin kasala. Lokacin mutuwata na matsowa. Ka da ku yi kuka, ba na son hawaye... Kun san ni, duk inda na je, zan kasance cikin farin ciki."

Maria Brayans ta shiga littafin tarihi

Kafar labaran Reuters ta ruwaito cewa diyar Maria ce ke kula da shafinsa X na dattijuwar.

Kara karanta wannan

Yunwa: Marayu 5 da mahaifiyarsu sun kwanta dama a Kano

A ranar 4 ga watan Maris ne shafin ba da kambu na duniya (GWR) ya sanar da cewa Maria ta cika shekara 117, wadda ta zamo mutum mafi tsufa a duniya daga Janairu 2023.

Wanda aka haifa a San Francisco, California a 1907, Maria ta yi kaura zuwa Cataloniya tare da ahalinta 'yan Sifaniya a lokacin ta na da shekaru bakwai.

An ce a Cataloniya ne yakin duniya na 1936-39 ya riski Maria, kuma ta tsallake annoba biyu da suka wakana na murar tsuntsaye ta Sigen a 1918 da annobar COVID-19 a 2020-2021.

Mace mafi tsayi a duniya ta rasu

A wani labarin, mun ruwaito cewa matar da ta fi kowa tsayi a duniya, wadda ta yi suna a matsayin 'sarauniyar tsawo' ta rasu a asibiti tana da shekaru 77.

Maria Feliciana dos Santos, 'yar Brazil, wacce ta ajiye tarihi, ta kara tsayi zuwa inci 87.8 a lokacin da shiga shekaru ashirin na rayuwarta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.