Matar da Tafi KOwa Tsufa a Duniya ta Mutu a Birnin Toulon

Matar da Tafi KOwa Tsufa a Duniya ta Mutu a Birnin Toulon

  • Sister Andre mai asalin suna Lucile Randon 'yar asalin kasar Faransa ita ce 'dan Adama mafi tsufa a yanzu a duniya, kuma ta mutu tana da shekaru 118
  • Ta kafa tarihin zama mutum mafi tsufa a duniya da ta taba kamuwa da cutar korona a 2021 kuma ta warke sarai, wanda littafin Guinness ya shaida
  • Kamar yadda tarihin rayuwarta ya nuna, bata taba shiga lamurran addini ba har sai da ta kai shekaru sama da 40 kuma malamar makaranta ce

Matar da ta kasance 'dan Adam mafi tsufa a duniya mai suna Andre, ta rasu tana da shekaru dari da goma sha takwas a kudancin birnin Faransa mai suna Toulon, sarkin birnin Hubert Falco ya sanar ranar Laraba.

Sister Andre
Matar da Tafi KOwa Tsufa a Duniya ta Mutu a Birnin Toulon. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: UGC

An haifeta a kudancin birnin Ales na Faransa a ranar 11 ga watan Fabrairun 1904 matsayin Lucile Randon, Andre a saka ta cikin jerin mutanen da suka fi kowa tsufa a duniya a wataan Afirilun 2022 a binciken da kungiyar Gerontology Research tayi.

Kara karanta wannan

Matashi ya Lakadawa Mahaifiyarsa Dukan Kisa Kan Rabon Gado, Tace ga Garinku a Delta

Matar 'yar asalin Faransa tayi aiki matsayin malama a yayin kuruciyarta kuma ba ta shiga wata al'umma ta addini ba har sai da ta kai shekaru 40 zuwa sama.

A cikin kwanakin nan ne ta fara amfani da keken guragu kuma na tsawon shekaru ta daina gani da idonta, jaridar The Nation ta rahoto.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

'Yar kasa ce da aka karrama a Toulon inda ta ke rayuwa a gidan wadanda suka yi ritaya na tsawon shekaru.

Daily Trust ta rahoto cewa, Falco ya yaba mata matsayin mace ta zamani kuma mai bauta da ke da zuciyar kirki.

Guinness World Records yace Lucile, wacce ta samu sunan Sister Andre a 1994 ita ce mutum ta biyu mafi tsufa 'yar kasar Faransa da kuma mafi tsufa ta biyu a Turai da suka taba shiga tarihin nan.

Kara karanta wannan

Komai ya kone: Gobara ta yi kaca-kaca da kayan miliyoyi a gonar fitacciyar jigo a Najeriya

A baya-bayan nan, Sister Andre ta karba yabon zama mutum mafi tsufa a duniya da ta kamu da cutar Korona a duniya kuma ta warke a 2021.

"Abun matukar mamaki ne a ce mutumin da aka haifa kafin zuwan robobo, zif da rigar mama duk yana raye kar karni na 21 kuma ya kamu da korona har ya tashi."

- Editan littafin tarihi na duniya na Guinness, Craig Glenday yace a wata takarda.

"Ni kaina karamci ne a wurina in rubuta labarinta a shafukan littafin kafa tarihin duniya na Guinness, kuma ta na raye matsayin mutum ta hudu mafi tsufa a duniya da aka tabbatar."

Da mutuwarta, Maria Branyas Morera, wacce ka rayuwa a kasar Spain, ta karba kambin inda ta zama mutum mafi tsufa a tarihin duniya mai shekaru 115 da ke rayuwa.

Daliba ta kafa kasuwanci da kudin makarantar ta

A wani labari na daban, wata budurwa ta bayyana kafuwar kasuwancinta bayan shekaru uku da ta kwashe kudin makarantar ta ta kafa shi.

Ta bayyana katafaren ofishinta inda ta sanar da cewa tana kwance kan gadon makaranta dabarar ta fado mata kuma ta aiwatar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel