Malawi: Jirgin Mataimakin Shugaban Ƙasa Ya Yi Hatsari, Mutanen Ciki Sun Mutu
- Rahotanni na nuni da cewa jirgin mataimakin shugaban kasar Malawi, Saulos Klaus Chilima ya yi hatsari dauke da mutane tara
- Shugaban kasar Malawi, Lazarus Chakwera ne ya fitar da sanarwar yana mai cewa Saulos Chilima da mutanen sun mutu a hatsarin
- A jiya Litinin ne muka ruwaito maku cewa jirgin sojojin Malawi, dauke da Chilima ya bace a sararin samaniya, kuma an gaza gano shi
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Malawi - Mataimakin shugaban kasar Malawi, Saulos Klaus Chilima da wasu mutane tara sun mutu a lokacin da jirgin sojin da suke tafiya a ciki ya yi hatsari.
Jirgin da ke dauke da Chilima, wanda ake ganin zai iya tsayawa takara a zaben shugaban kasa na badi, ya bace a ranar Litinin.
Mataimakin shugaban kasar Malawi ya mutu
Shugaban kasar Malawi, Lazarus Chakwera ne ya fitar da sanarwar mutuwar mataimakin na shi a ranar Talata kamar yadda shafin Reuters ya ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Ina mai bakin cikin sanar da ku cewa mummunan abin da muke addu'ar kar ya faru, shi ne ya faru. Tawagar bincike da ceto sun gano jirgin a kusa da wani tsauni.
"Sun gano cewa babu wanda ya tsira daga wannan hatsarin sakamakon yadda jirgin ya tarwatse tare da komawa tarkace."
- Lazarus Chakwera
Shugaba Chakwera ya shaida haka a wani jawabin kai tsaye ga al'ummar kasar Malawi.
"Wani abu ya faru da jirgin" - Shugaban Malawi
Jaridar BBC ta ruwaito Chakwera na cewa dukkanin fasinjojin da ke cikin jirgin sun mutu ne sakamakon hatsarin da ya faru kuma sojoji na hanyar dawo wa da gawarwakinsu.
Shugaban kasar ya ce:
"Duk da bin diddigi da kuma kwarewar ma'aikatan jirgin, wani mummunan abu ya faru da jirgin a lokacin da ya ke hanyar komawa Lilongwe, wanda ya sa ya yi hatsari."
Jirgin Saulos Chilima ya bace a Malawi
Tun da fari, mun ruwaito cewa jirgin da ke dauke da mataimakin shugaban kasar Malawi, Saulos Klaus Chilima ya bace a ranar Litinin, 10 ga watan Yunin 2024.
An ce jirgin ya tashi daga Lilongwe, babban birnin kasar da misalin karfe 9:00 na safiya da zummar zai sauka babbar tashar jiragen sama ta Mzuzu da misalin karfe 10:00 na safiyar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng