Allah Mai Iko: Jerin Sunayen Ƙasashen Duniya 6 da Rana Ba Ta Faɗuwa Na Tsawon Lokaci Ba Dare

Allah Mai Iko: Jerin Sunayen Ƙasashen Duniya 6 da Rana Ba Ta Faɗuwa Na Tsawon Lokaci Ba Dare

  • Akwai wasu kasashe shida a faɗin duniya da Allah ke ikonsa, inda rana ke shafe tsawon lokaci ba ta faɗi ba
  • Kasar Sweden da Finland na daga cikin jerin waɗannan kasashe, inda kuma ake samun wasu lokuta da ake samun dare na tsawon lokaci
  • Waɗannan ƙasashe na ganin iko na Ubangijin da ya halicci kowa, kuma a haka mutane ke rayuwa a wuraren

Sweden - Ƙasahen turawa, Finland da Sweden na daga cikin jerin ƙasashen duniya shida, waɗanda rana bata faɗuwa na tsawon wani lokaci.

Punch ta ruwaito cewa waɗan nan kasashen na fuskantar zafin rana na tsawon watanni ba tare da ta faɗi ba kuma wasu na fuskantar duhun dare na yan kwanaki.

Legit.ng Hausa ta tattaro muku waɗannan kasashe:

Kara karanta wannan

Faɗawa Shugaba Gaskiya Yanzun Ya Zama Sabon Matsalar Tsaro a Najeriya, Malamin Addini Ya Magantu

Sweden

Ƙasar Sweden dake yankin turawa, tana fuskantar rana ba tare da ta faɗuwa ba na tsawon watanni shida a kowace shekara.

Tun daga farkon watan Mayu, har zuwa ƙarshen watan Agusta, rana tana faɗuwa ne da tsakiyar dare kuma ta sake fitowa da ƙarfe 4:00 na asubahi.

Sweden
Allah Mai Iko: Jerin Sunayen Ƙasashen Duniya 6 da Rana Ba Ta Faɗuwa Na Tsawon Lokaci Ba Dare Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Finland

A lokacin damina, a mafi yawancin yankuna ƙasar Finland rana bata faɗuwa kwata-kwata na tsawon kwanaki 73

Amma a lokacin hunturu ba'a ganin ko da ɗigon hasken rana a baki ɗaya sassan kasar.

Norway

Ana kwashe kwanaki 76 a ƙasar Norway ba tare da rana ta faɗi ba, kuma ana kiran ƙasar da ƙasar rana.

Tun daka watan Mayu zuwa ƙarshen watan Yuli, kasar na shan hasken rana ba tare da faɗuwa ba.

Nunavut, Canada

Birnin Nunavut dake arewa maso yammacin ƙasar Canada, na fama da hasken rana na tsawon watanni biyu ba tare duhun dare ya gitta ba.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Shahararren Ɗan Kasuwa Ya Maka Tsohuwar Matarsa a Kotun Musulunci Kan Jaririn da Ta Haifa

Amma a lokacin damuna, birnin na fusakantar duhun dare na tsawon kwanaki 30.

Iceland

Bayan ƙaurin sunan da Iceland ta yi na ƙasar da babu sauro kwata-kwata. A lokacin sanyi ana dare ne kawai a ƙasar yayin da rana bata faɗuwa a watan Yuni.

Barrow, Alaska

Rana ba ta faɗuwa a wannan yankin tun daga ƙarshen watan Mayu har zuwa karshen daren watan Yuli.

Hakazalika daga farkon watan Nuwamba, rana bata fitowa sam har tsawon kwanaki 30 a jere, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kakin ku zai iya kaiku wuta ko Aljanna - IGP

A wani labarin na daban kuma sufetan yan sandan ƙasar nan ya shaidawa yan sanda cewa da aikinsu zasu iya shiga Aljanna ko Wuta

Sufetan yan sanda, Usman Alkali Baba, ya yabawa jami'an yan sanda dake aiki a jihar Kwara bisa namijin kokarin da suke wajen tabbatar da tsaro.

IGP ya shaidawa jami'an cewa wannan aikin da suke na al'umma ne, zai iya jefa su cikin aljanna ko wuta ranar kiyama.

Kara karanta wannan

Bayan Kwana 100 da Hana Hawa Twitter, Rahoto Ya Bayyana Biliyoyin Nairorin da Najeriya Ta Yi Asara

Asali: Legit.ng

Online view pixel