Kungiyar Farar Hula Ta Soki Shugaban ’Yan Sanda Kan Kalaman Hada Jami’ansa da NCDC
- Yayin da aka shiga watan Shawwal, kasar Saudiyya ta sanar da cewa ta kammala shirye-shiryen fara karban baki domin fara aikin Hajjin bana
- Sanarwar wanda ta fito daga hukumomin kasar ta nuna cewa yau Laraba ne za a fara gudanar da ayyukan hajji a wannan shekarar
- Wannan rahoton ya kun shi bayani a kan irin shirin da Saudiyya ta yi da kuma wasu abubuwa na musamman da suka shafi aikin hajji
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
A yayin da ake shirin fara aikin Hajjin shekarar 2024, kasar Saudiyya ta fitar da sanarwar cewa ta shirya tsaf domin fara karbar alhazai
Shirin fara aikin hajjin shekarar 1445
A cikin sanarwar, hukumomin a kasar sun tabbatar da cewa a yau Laraba, 24 watan Afrilu ne za a fara gudanar da ayyukan hajjin bana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta fito ne daga shafin Facebook na kasar mai suna Inside the Haramain. Ga abin da sanarwar ta kunsa:
"Hajjin shekarar 1445/2024 zai fara a yau.
Masallacin Makka da Madinah da sauran wurare masu alfarma a garin Makka sun fara shirye-shiryen karban alhazai domin gudanar da aikin hajjin bana"
Watannin aikin hajji
Akwai watanni uku da shari'ar Musulunci ta ware da ake gudanar da aikin hajji a cikinsu. A shafin fatawa na IslamicQnA, babban malamin addinin Musulunci Sheikh Salih Al-Munajjid ya bayyana cewa watannin su ne:
1. Shawwal, watan 10
2. Zul Qidah, watan 11
3. Zul Hijja, watan 12
A cewar malamin dukkan ayyukan aikin hajji ana fara su da kammala su ne a cikin watannin, idan mutum ya yi ba a cikin su ba to aikinsa bai cika ka'ida ba.
Ladubban aikin hajji a musulunci
Har ila yau, Sheikh Salih Al-Munajjid ya kara da cewa aikin hajji yana cike da wasu irin laduba da ake so a aikata su.
Daga ciki ya lissafa cewa ana bukatar mai aikin hajji ya yi kokarin wurin taimakon sauran mahajjata da kuma tausaya musu.
A cewarsa, taimakon yana da muhimmanci musamman a wuraren da suke da cinkoso. Kuma ya kara da cewa idan mutum ya tausaya ma wasu shima Allah zai tausaya masa.
Ya kuma kara da cewa ana so mai aikin hajji ya nisanci ayyuka munana da fasikanci. Kuma ba a so mutum ya zama mai kaushin hali ga 'yan uwansa mahajjata.
Shehin ya kuma ce ana so ya nisanci yin gulma da zagi da kalle-kallen mata ko zaluntar wasu mahajjatan a lokacin da ya fara aikin.
An kara kudin aikin hajji a Najeriya
A wani rahoton kuma kun ji cewa, hukumar kula da Alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta ƙara kuɗin zuwa aikin hajjin bana a ƙasar Saudiyya da N1,918,032.91.
Mai magana da yawun hukumar NAHCON, Fatima Sanda Usara, ta sanar da hakan, inda ta bayyana cewa hakan ya faru ne saboda tashin dala
Asali: Legit.ng