An ji karar fashewar wani abu a, Riyadh, babban birnin Saudiyya

An ji karar fashewar wani abu a, Riyadh, babban birnin Saudiyya

- An ji karar fashewar wani abu a Riyadh, babban birnin kasar Saudi Arabia a ranar Asabar

- Gidan talabijin na Saudiyya, Al Arabiya TV ya ruwaito cewa an samu fashewar wani abun fashewa

- Dakarun sojojin hadin gwiwa karkashin sojojin Saudiyya da ke Yemen sun ce sun dakile wani hari da aka yi nufin kaiwa Riyadh a ranar Asabar

An ji karar fashewar wani abu a babban birnin kasar Saudiyya wato Riyadh a ranar Talata 26 ga watan Janairun shekarar 2021 a cewar wakilin kafar watsa labarai na Reuters.

Sai dai ba a tabbatar da sababin karar ba nan take, Premium Times ta ruwaito.

An ji karar fashewar wani abu a, Riyadh, babban birnin Saudiyya
An ji karar fashewar wani abu a, Riyadh, babban birnin Saudiyya. Hoto daga @PremiumTimesNg
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yanzu Yanzu: An cinnawa gidan Sunday Igboho wuta a Ibadan (Hotuna)

Gidan talabijin mallakar Saudiyya ta Al Arabiya TV ya ruwaito cewa an samu fashewar wani abu da bidiyon da ke nuna cewa hukumomin kasar sun dakile wani makami mai linzami da ya biyo da sararin samaniyar Riyadh da ke yawo a dandalin sada zumunta.

KU KARANTA: Wata mata ta sheƙawa kishiyarta tafasasshen ruwan zafi a Kano

A ranar Asabar, sojojin hadin gwiwa karkashin dakarun sojojin kasar Saudiyya da ke Yemen sun ce sun dakile wani harin da makiya suka yi nufin kai wa birnin Riyadh sun kuma lalata makamin da aka aiko.

A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.

An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.

Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel