Kasar Amurka Ta Gargadi Isra’ila Kan Sake Takalo Takaddama da Iran

Kasar Amurka Ta Gargadi Isra’ila Kan Sake Takalo Takaddama da Iran

  • A wani sako da ta aikawa Isara'ila, Amurka ta bayyana cewa ba za ta taya Isara'ila yaki da Iran ba idan ta kuskura ta sake tsokano fadan
  • Har ila yau kasar ta Amurka ta bayyana manyan dalilai kan daukan matakin kin taya Isra'ila yaki da Iran
  • Jami'an tsaron Amurka sun tabbatar da aike wannan sako zuwa ga Isara'ila ta ganawar sirri ta wayar tarho a ranar Lahadi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Yayin da kasar Isra'ila ke nazarin mayar da martani game da harin da Iran ta kai mata karshen mako, Amurka ta aike mata da wani sako mai ban takaici da sanyaya gwiwa.

Kara karanta wannan

Innalillahi: An yi wa yarinya 'yar shekara 10 kisan gilla a wani birnin Arewacin Najeriya

Kasar Amurka ta bayyana a cikin wata tattaunawa ta sirri cewa idan Isra'ila ta zabi mayar da martani ta hanyar soji, to Amurka ba za ta mara mata baya ba.

Iran v Israila
Iran ta kai harin ramakon gayya wa Isra'ila a karshen mako. Hoto: Contributor, Sean Gallup
Asali: Getty Images

Dalilin da ya sa Amurka nokewa

Gwamnatin shugaba Biden ta bayyana karara cewa Amurka ba za ta bada gudunmawa kan kai hare-haren soji kan Iran ba saboda fargabar barkewar yaki a gabas ta tsakiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wani babban jami’in gwamnatin Amurka ya shaida cewa sunyi imanin Isra’ila na da ‘yancin daukar mataki don kare kanta amma ba za su taya ta yaki da Iran ba.

Amurka ta aika sako ga Isra'ila.

A wani rahoton da jaridar ABC News ta ruwaito kuma, wani jami'in Amurka ya tabbatar da cewa an isar da sakon cewa Amurka ba za ta taya Isara'ila yaki da Iran ba kai tsaye ga manyan jami'an Isra'ila.

Kara karanta wannan

Rudin soyayya: Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da jami'inta ya kashe mace mai ciki

Hakan ya faru ne a wata ganawar sirri ta wayar tarho a ranar Lahadi tsakanin sakataren tsaron Amurka, Lloyd Austin, da ministan tsaron, Isra'ila Yoav Gallant.

Harin da Iran ta kai

Harin da Iran ta kai Isra’ila ya samu kakkausar suka daga shugabannin duniya, ciki har da jami’an Amurka wadanda da farko suka yi tunanin Iran ta shirya makami mai linzami guda 12 ne kacal.

Wani babban jami’in Amurka ya bayyana yana rawar jiki a yayin da yake daukar bayanai a wani taro da suka gano cewa Iran ta shirya harba makamai masu linzami fiye da 100 zuwa Isara'ila.

An dauki harin a matsayin ramuwar gayya ga harin da aka kai karamin ofishin jakadancin Iran da ke Damascus na kasar Syria, wanda ake kyautata zaton Isra'ila ne ta kai.

Iran ta gargadi Isra'ila

A wani rahoton kuma, kun ji cewa yayin da ake ci gaba da rikici tsakanin isra'ila da Hamas, Iran ta yi gargadi ga kasar kan mamayar Gaza.

Ministan harkokin wajen Iran, Hossien Amir-Abdollahian ya bayyana haka yayin da sojin Isra'ila su ka shirya mamayar Zirin Gaza.

Asali: Legit.ng

Online view pixel