Hotunan Diyar Jackie Chan Tana Rayuwa Cikin Fatara a Canada Sun Bayyana

Hotunan Diyar Jackie Chan Tana Rayuwa Cikin Fatara a Canada Sun Bayyana

  • Duk da dukiyar da ta kai $400 miliyan da ya mallaka a duniya, diyar Jackie Chan, Etta Ng Chok tana rayuwa cikin matsanancin talauci inda take rokon abinci
  • Ng diyar Chan ce wacce ya haifa da masoyiyarsa tsohuwar sarauniyar kyau amma bai taba ganawa da ita ba kuma bai taba daukar nauyinta ba
  • Matashiyar budurwar mai shekaru 22 an gan ta tana barar abinci a Toronto bayan ta bar makaranta tare da tserewa da saurayinta

Etta Ng Chok, diyar jarumin fim din China Jackie Chan Kong-sang an gan ta tana layin bara domin karbar abinci a Toronto duk da mahaifinta yana da dukiyar da ta kai $400 miliyan.

Jackie Chan
Hotunan Diyar Jackie Chan Tana Rayuwa Cikin Fatara a Canada Sun Bayyana. Hoto daga Jackie Chan, The Standard
Asali: UGC

Hotunan Ng dake yawo a kafar sada zumuntar zamani ya bayyanata tana layin karbar abincin sadaka tare da wasu tsofaffin mata a ranar 9 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

An Samu Jihar Farko a Arewa da ta fara Cin Dukiyar Fetur Bayan Gano Danyen Mai

Matashiyar budurwar mai shekaru 22 an ganta sanye da wata riga mai tsawo da dogon wando tare da wasu takalma marasa kyan gani.

The Standard sun rahoto cewa, tayi kalar talauci kuma babu kyan gani. Ma’abota amfani da kafafen sada zumuntar zamani sun ce tayi kama da wacce bata da gidan zama.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ng ta taho da katuwar jakar leda wacce zata yi amfani da ita wurin karbar abincin sadakar.

Ng diyar Jackie Chan ce ta soyayya da Elaine Ng Yi-lei. Alakarsa da mahaifiyar tayi tsaro ne bayan matashiyar ta bar makaranta kuma ta gudu da masoyinta, fitaccen ‘dan soshiyal midiya na kasar Canada mai suna Andi Autumnin a 2017.

Jim kadan kafin aurensu, Ng da Autumn sun wallafa bidiyonsu mai bada mamaki a YouTube inda suka yi ikirarin cewa basu da gida kuma suna kwana a kasan gada sakamakon tsangwamar iyaye.

Kara karanta wannan

Wasu Shugabannin PDP na Neman Tada Rikici, Sun ce An Ware Su a Yakin Zaben Atiku

“Ban fahimci me ke faruwa ba saboda mun je wurin ‘yan sanda, mun je asibiti, wurin bada abinci, mazaunin masu auren jinsi kuma dukkansu basu damu ba.”

- Ng tace a bidiyon da yanzu aka goge.

Masoyan junan sun yi aure a Canada a shekarar 2018 kuma Style Reports ta bayyana cewa Chan yana auren jarumar fim din Taiwan Joan Lin amma a 1999 ya amsa cewa yayi harka da Elaine Ng Yi-lei, sarauniyar kyau.

Duk da a fili ya bayyana cewa sarauniyar kyan nahiyar Asiya ta 1990 din tana da ciki, bai taba daukan dawainiyar abinda ta haifa ba.

Har Masu Zundena Kan Kwasar Bola da Nake yi Sun bi Sahu na: Tsohuwa Mai Shekaru 63

A wani labari na daban, Amdalat Taiwo Pedro mata ce da mijinta ya mutu amma take sana’ar kwashe bola a titinan Legas a kokarinta na samun abinda zata ci da kuma kula da kanta.

Sakamakon hauhawar farashi da tsananta rayuwa a kasar, mutane da yawa sun kama sana’o’i wadanda a baya ba zasu taba yin su ba, BBC News ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel