Innalillahi: An Yi Wa Yarinya ’Yar Shekara 10 Kisan Gilla a Birnin Arewacin Najeriya

Innalillahi: An Yi Wa Yarinya ’Yar Shekara 10 Kisan Gilla a Birnin Arewacin Najeriya

  • An yi wa wata yarinya mai suna Glory 'yar shekara 10 kisan gilla a karamar hukumar Birnin Kebbi a jihar Kebbi a dakin mahaifiyarta
  • Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa kallo na karshe da aka yi wa yarinyar shi ne lokacin da mahaifiyarta ta aike ta share mata daki
  • Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kebbi, SP Nafiu Abubakar, ya bayyana matsayin hukumar 'yan sanda a kan lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kebbi - Rahotannin da muke samu sun bayyana cewa, an yi wa wata yarinya ‘yar shekara 10 mai suna Glory kisan gilla a garin Birnin Kebbi na jihar Kebbi.

Kara karanta wannan

Rudin soyayya: Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da jami'inta ya kashe mace mai ciki

Wani makwabcinsu a unguwar Badariya ya shaida cewa kallo na karshe da aka yi wa yarinyar shine lokacin da take wasa a wajen gidansu sai mahaifiyarta ta ce ta je ta share mata daki.

Gwamnan jihar Kebbi
An yi wa yarainya 'yar shekara 10 kisan gilla a Birnin Kebbi. Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

Ya cigaba da cewa, a lokacin da yarinyar ba ta dawo kan lokaci ba, sai mahaifiyar ta aika kanwarta mai kimanin shekara biyar ta kira ta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Halin da aka samu Glory

Lokacin da kanwarta ta shiga dakin sai ta same ta tana rike da wuyanta da igiya an shake ta da karfen tagar dakin

Mahaifiyar yarinyar ta ce yadda aka kasheta ya zo musu da mamaki. Saboda babu wanda ya yi tsammanin za a yi kisan gilla ga yarinya mai wannan shekarun na ta.

Matakin da mahaifiyar ta dauka

Mahaifiyar ta tabbatar wa jaridar Daily Trust cewa an kai rahoton lamarin a ofishin ‘yan sanda domin bincike da daukan matakin da ya dace.

Kara karanta wannan

Kano: Abba Kabir ya dauki zafi bayan sakin 'yan daba daga kulle, ya sha alwashi kan lamarin

Sannan kuma an kai gawarta kauyen iyayenta da ke karamar hukumar Zuru domin binne ta a can.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Nafiu Abubakar, ya ce har yanzu ba a yi masa bayani kan lamarin ba.

An yiwa malami kisan gilla

A wani rahoton kuma, kun ji cewa a ranar Talata ce 5 ga watan Maris aka yi wa wani malamin addini kisan gilla mai suna Abubakar Hassan Mada a jihar Zamfara.

Ana zargin wasu 'yan sa kai da ke hukumar CPG da kisan malamin a garin Mada da ke Gusau a jihar Zamfara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel