An Bude Shagunan Kwankwaɗar Barasa Na Farko a Riyadh Ta Kasar Saudiyya

An Bude Shagunan Kwankwaɗar Barasa Na Farko a Riyadh Ta Kasar Saudiyya

  • A karon farko, tun bayan shekaru 70, kasar Saudiya ta bude shagunan shan barasa a birnin Riyadh
  • Saudiyya ta dauki wannan mataki ne domin ba baƙi jakadun kasashen waje damar shan barasa a birnin
  • Legit Hausa ta ji ta bakin malamin addini kuma Lakcara a Jami'ar Tarayya ta Kashere da ke jihar Gombe

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Riyal, Saudiyya - Hukumomi a kasar Saudiyya sun bude shagunan shan barasa a birnin Riyadh da ke kasar.

Wannan mataki shi ne irinsa ba farko a kasar kusan shekaru 70 da suka wuce ba tare da ba da wannan damar ba.

Saudiyya ta bude shagunan shan barasa a karon farko
Saudiyya ta bude shagunan shan barasa domin baki 'yan kasashen waje. Hoto: Chesnot.
Asali: Getty Images

Dalilin bude shagunan shan barasa a Saudiyya

Saudiyya kasa ce ta Musulunci da aka haramta shan barasa ko siyar da ita saboda bin tsarin addinin Musulunci.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Bola Tinubu ta gurfanar da shugaban kungiyar Fulani ta Miyetti Allah, Bodejo

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai an bude shagunan ne saboda jami'an jakadancin kasashen ketare da ke kawo ziyara kasar, cewar BBC Hausa.

Kasar ta sha suka tun a shekarun bayan kan matakin hana shan barasa inda wasu ke ganin ta tauye hakkin dan Adam.

Wannan na zuwa ne bayan kasar ta sanar a watan Janairu cewa za ta buɗe wasu shagunan shan barasa saboda baki 'yan kasashen waje.

Tsoron da mutane ke yi kan matakin

Sanarwar ta ce za ta siyar da barasar ce ga mutane wadanda ba Musulmai ba a birnin Riyal, The Current ta tattaro.

Wannan mataki na Saudiya ya saka shakku a zukatan Musulmi da dama ganin yadda ake sassauta irin wadannan dokoki a kasar.

Wasu na ganin hakan zai kara bude kofofin barna a kasar wurin ba da damar aikata ayyukan da ba su dace ba a kasar da ake ganinta mai tsarki.

Kara karanta wannan

Kano: Sabuwar takaddama ta taso yayin da 'yan sanda suka bukaci diyya daga Murja Kunya

Legit Hausa ta ji ta bakin malamin addini kuma Lakcara a Jami'ar Tarayya ta Kashere da ke jihar Gombe

Malam Muhammad Umar ya yi Allah wadai da wannan mataki inda ya ce alamun tashin duniya ne.

"Wannan abin da ya faru a Saudiya sai dai muce Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, ita giya ko ba Musulmi ba, da mai siyarwa da wanda ya siya Allah ya raine musu albarka."
"Wannan abin bakin ciki ne ga duk wani Musulmi, to sai dai Allah ya ce duk ƙasar da saba masa, masifa za ta iya hawa kanta."

- Mallam Muhammad Umar

Ya ce duk arzikin da Saudiyya ke da shi idan aka ci gaba da sabon Allah, Ubangiji zai ƙaryata kuma ya mayar da ita aya ga Musulmi.

Ya kara da cewa da zarar Saudiyya ta lalace hakan ya na nuna alamu ne na tashin duniya.

Saudiyya ta haramta Umrah sau 2

Kara karanta wannan

Kotu ta yanke hukunci kan mutumin da ya sace Alkur'anai a Masallaci, ta ba shi zaɓi 1 a Abuja

Kun ji cewa Ma'aikatar Hajji da Umrah a Saudiyya ta fitar da wata sanarwa kan gudanar da Umrah sau biyu a Ramadan.

Hukumar ta kafa dokar ce ganin yadda masu buƙatar yin Umrah suka fi yawa a wannan watan Ramadan da muke ciki.

Dokar ta hana alhazai yin Umrah sau biyu ko fiye da haka a cikin watan Ramadan domin rage cunkuson jama'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.