Saudiyya Za Ta Bai Wa Baki Damar Siyan Giya, Ta Bayyana Babban Dalilin Sabunta Dokar

Saudiyya Za Ta Bai Wa Baki Damar Siyan Giya, Ta Bayyana Babban Dalilin Sabunta Dokar

  • Saudiyya za ta sake sabunta dokar ta’ammali da giya a kasar musamman ga baki wadanda ba Musulmai ba
  • Dokar za ta bai wa bakin wadanda ba Musulmai ba damar siyan giyar wanda a baya aka haramta musu
  • Kafin kawo wannan doka, baki ‘yan kasashen waje suna shigo da giyar ce ta hanyoyin da ba su dace ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Riyad, Saudiyya – Kasar Musulunci ta Saudiyya za ta bayar da damar siyar da giya ga baki ‘yan kasashen waje.

Rahoton Channels TV ya tattaro cewa za a bayar da damar ce ga wadanda suka zo bakonta kasar kuma wadanda ba Musulmai ba.

Bayan dokar hana siyar da giya, Saudiyya ta bude babban shagon siyar da ita
Daga Karshe, Saudiyya Za Ta Sabunta Dokar Hana Baki Damar Siyan Giya. Hoto: Chesnot.
Asali: Getty Images

Wace doka ke aiki a baya a Saudiyya?

Kara karanta wannan

Mata da miji sunyi karyar yan bindiga sun sace su domin dangi su musu karo-karon naira miliyan 5

Kafin kawo wannan doka, baki ‘yan kasashen waje suna shigo da giyar ce ta ofishin jakadunsu a matsayin sako.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An hana siyar da giyar ce a Saudiyya tun 1952 jim kadan bayan dan Sarki Abdul’aziz ya yi tatil tare da harbe wani dan Burtaniya.

An yi ta yada jita-jita tun shekarun baya cewa giyar za ta zama abin banza a kasar ganin yadda ake ta kawo sauye-sauye a Saudiyya.

Sarki Muhammad Bin Salman ya kawo sauye-sauye wadanda suka hada da samar da gidajen sinima da kuma gidajen rawa tsakanin maza da mata.

Kasar ta fitar da wata sanarwa a yau Laraba 24 ga watan Janairu inda ta ce ta kafa wasu dokoki da zai rage siye da siyar da giyar ba bisa ka’ida ba.

Sanarwar da kasar ta fitar

Sanarwar ta ce:

Kara karanta wannan

Mahara sun shiga jami'ar BUK Kano sun yi garkuwa da ɗalibai? Gaskiya ta bayyana

“Sabuwar dokar za ta tabbatar an samar da kayyadadden giya ga baki yayin shiga kasar don rage yawan yaduwarta ba bisa ka’ida ba.
“Sannan dokar za ta dakile yawan siyar da giyar ta hanyar da ba ta dace ba a cikin kasar baki daya.”

A dokar Saudiyya, duk wanda aka kama da laifin siyar da giya ko samar da ita zai fuskanci dauri a gidan kaso da bulala, cewar Reuters.

Sannan idan ya kasance bako ne a kasar ya aikata haka, hukumomi za su dauki matakin korar shi a kasar.

Dalilin kashe kudade da Saudi ke yi a wasanni

A wani labarin, ganin yadda Saudiyya ke zuba makudan kudade a harkar wasanni, abin ya fara jawo cece-kuce.

Sai dai an bayyana ainihin dalilin zuba makudan kudaden a harkokin wasanni da cewa na daga cikin muradun 2022 na kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.