Facebook: Elon Musk Ya Tsokani Zuckerberg Bayan Samun Tangarɗa a Shafukansa, an Yi Korafi

Facebook: Elon Musk Ya Tsokani Zuckerberg Bayan Samun Tangarɗa a Shafukansa, an Yi Korafi

  • Miliyoyin mutane da dama sun samu matsala da shafukansu na Facebook da Instagram a yammacin yau Talata
  • An samu matsalar ce bayan daukewar shafukan guda biyu wadanda ke karkashin kamfanin Meta a fadin duniya gaba daya
  • Mai kamfanin X wanda aka fi sani da Twitter, Elon Musk ya yi shagube ga kamfanin Meta kan tangardar da aka samu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Mamallakin kamfanin X wanda aka fi sani da Twitter, Elon Musk ya yi martani bayan daukewar shafukan Facebook da Instagram.

Musk ya yi shagube ga kamfanin Meta wanda dukkan shafukan biyu ke karkashinsa inda suka shafe kusan awa a bace.

Musk ya yi martani bayan daukewar Facebook da Instagram
Musk ya yi shagube ga Mark Zuckerberg kan lalacewar Facebook da Instagram. Hoto: @elonmusk, @zuck/Threads.
Asali: Twitter

Wane martani Musk ya yi kan Facebook?

Kara karanta wannan

Kamfanin Meta ya magantu bayan daukewar Facebook, Messenger da Instagram

Musk wanda ya ke takun saka da mai kamfanin Meta, Mark Zuckerberg ya bayyana haka a shafinsa na X a yammacin yau Talata 5 ga watan Maris.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Idan kana karanta abin da na wallafa yanzu, ya na nufin manhajarmu ta X ta na aiki kenan.”

- Elon Musk

Wannan wallafar na nufin shafukan Facebook da Instagram na kamfanin Meta sun dauke yayin da X ke aiki a wannan lokaci.

Musk da Mark abokanan hamayya ne wadanda suka sha takun saka saboda harkar kasuwanci ta hada su tare.

Menene ya faru da Facebook da Instagram?

A yammacin yau Talata ce 5 ga watan Maris aka samu tangarda a kafofin sadarwa ta Facebook da Instagram a fadin duniya.

Reuters ta tattaro cewa wata kafa da ke bincikar irin wannan matsala mai suna Downdetector.com ta tabbatar da faruwar lamarin.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Tun da muka tsallake ƙangin mulkin Buhari a 1984, wannan ma zai wuce, malamin addini

Kafar ta tabbatar da cewa miliyoyin mutane a duniya sun gagara ziyarar shafukansu na Facebook da Instagram dalilin haka.

Tangardar da aka samu ta jawo cece-kuce inda wasu suka koma shafukansu na X domin ci gaba da samun labarai da sauran harkokinsu.

Meta ta yi martani kan samun matsala

Kun ji cewa a yammacin yau Talata 5 ga watan Maris aka samu matsala a shafukan Facebook da Instagram.

Dukkan shafukan na karkashin kamfanin Meta wanda Mark Zuckerberg ke jagoranta bayan siyansu da ya yi.

Kakakin kamfanin Meta wanda uwa ce ga Facebook da Instagram, Andy Stone ya bayyana dalilin a shafin X.

Asali: Legit.ng

Online view pixel