Dalilin da yasa mata suka fi son dogon namiji
- Tarihi ya nuna cewar mata sun fi son dogon namiji saboda wasu dalilai da suka banbanta daga mace zuwa mace.
- Duk da wadannan mabanbantan dalilai, akwai wasu da aka nazarci cewar mata sun yi tarayya a cikinsu
- Sai dai wani bincike na baya bayan nan ya nuna cewar halayyar mutum ta fi tasiri a wurin mata fiye da tsayi ko gajartar sa
Duk da bahaushe na cewa "soyayya gamon jini, da yawan mata sun fi son su yi soyayya ko aurar dogon namiji.
Daga cikin irin dalilan da yasa mata suka fi son dogon namiji akwai batun burgewa da kwarjini dake tattare da tsawo.
Wani binciken masana ya nuna cewar dogayen maza na da damar samun nasara a zabe fiye da gajeru kuma sun fi iya jagoranci a lokacin da suka samu mulki.
Kazalika, binciken masanan ya bayyana cewar mata sun fi son dogon namiji saboda bai cika nuna kishi ga 'yan uwansa maza ba, kamar yadda gajere ke nuna kishi a kan dogo ba.
Karin dalilin da wasu mata ke bayar wa shine batun kallon karfi da ake yiwa namiji. Mata da dama sun fi samun natsuwa da kwanciyar hankali idan ya kasance mijinsu dogo ne.
DUBA WANNAN: Biki bidiri: Hotunan bikin dan Sarki Sanusi II
Dadi da kari, wasu mata na ganin cewar dogon namiji yafi iya soyayya da kuma hakuri.
Sai dai duk wadannan dalilai da masana da matan suka bayyana, wani bincike na kwanan nan ya tabbatar da cewar halin mutum yafi tasiri a wurin mata fiye da tsawo ko gajartar sa.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng