Kasar Girka Ta Kuduri Aniyar Halatta Auren Jinsi, Da Daukar Rainon Yara

Kasar Girka Ta Kuduri Aniyar Halatta Auren Jinsi, Da Daukar Rainon Yara

  • Majalisar dokokin kasar Girka ta shirya ƙada kuri'a kan dokar halasta auren jinsi da ba masu auren damar rainon yara har su gaje su
  • Wannan kudin wanda Firayin Minista Kyriakos Mitsotakis da kansa ya gabatar, ya samu suka daga malaman addini da al'ummar kasar
  • Sai dai a hannu daya, kungiyar LGBTQ ta ce wannan dokar abar kauna ce, la'akari da yadda ake nuna tsana ga iyali masu auren jinsi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

A yau Alhamis ne majalisar dokokin kasar Girka za ta hallata auren jinsi da daukar rainon yara, wani gagarumin sauyi da gwamnati ta dauka kan adawar Cocin Orthodox na kasar.

Ana sa ran da yawa daga cikin 'yan majalisar dokokin jam'iyyar New Democracy mai mulki za su yi adawa da kudurin a kuri'ar da za a kada a yammacin ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari masallaci, sun kashe masallata 3 tare da sace wasu da dama a jihar Arewa

Firayim Minista Kyriakos Mitsotakis ya gabatar da kudurin halatta auren jinsi.
Firayim Minista Kyriakos Mitsotakis ya gabatar da kudurin halatta auren jinsi. Hoto: Michael Varaklas
Asali: AFP

Firayim Minista Kyriakos Mitsotakis, wanda shi da kansa ya jagoranci kudirin, ya bukaci 'yan majalisar da su "dage wajen kawar da rashin daidaito" a dimokuradiyyar Girka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyoyin LGBTQ sun yi maraba da dokar

Ya kara da cewa:

"Dokar za ta inganta rayuwar masu ha'awar auren jinsi ba tare da ta rage komai daga rayuwar mutane da yawa ba."

The Guardian ta ruwaito kungiyoyin LGBTQ suna yaba da kudirin a matsayin wani abu na tarihi. Sun ce ma'auratan jinsi daya na fuskantar wariya a karkashin dokar iyali ta yanzu.

A dul lokacin da 'ya'yansu suka kamu da rashin lafiya a Girka, iyayen kan rasa ikon yanke shawarar irin hanyoyin kiwon lafiya da yaran ke bukata a gare su.

Ga kuma dokar da ta hana yaran da ake riko su gaji dukiyar iyayen rukon su kai tsaye.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Tinubu ya ba jami'an tsaro umarnin cafke masu boye kayan abinci

Ikilisiya 'na adawa gaba daya da kudurin'

Kasar Girka za ta zama kasa ta farko ta Kiristan Orthodox, kasa ta 17 ta EU da kuma kasa ta 37 a duniya da ta halasta auren 'yan jinsi guda, New York Times ta ruwaito.

Cocin Girka wacce ke da kusanci da 'yan majalisar gwamnati da yawa ta ce tana adawa da wannan kudiri gaba daya tare da la'antar matakin.

Archbishop Ieronymos, shugaban cocin, ya soki dokar da aka gabatar a matsayin wani bangare na yunkurin aiwatar da "sabon abu da ke neman lalata haɗin kan zamantakewar kasar."

Kimanin mutane 4,000 ne suka gudanar da zanga-zangar adawa da matakin a birnin Athens a ranar Lahadin da ta gabata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.