Gawa Ta Ƙi Rami: Matar da Mijinta Ya Ayyana Cewa Ta Mutu Ta Buɗe Ido Ana Dab da Ƙona Ta

Gawa Ta Ƙi Rami: Matar da Mijinta Ya Ayyana Cewa Ta Mutu Ta Buɗe Ido Ana Dab da Ƙona Ta

  • Wata mata mai suna Bujji Aamma daga Berhampur, Indiya, ta bude ido ana dab da kona ta bayan da aka yi tunanin ta mutu
  • Rahotanni sun bayyana cewa Aamma ta kone sosai a wata gobarar gida a ranar 1 ga Fabrairu, amma saboda rashin kudi ba a barta a asibiti ba
  • Dakin kona gawar sun ce ana samun irin wannan abun saboda mutanen garin ba sa bukatar shaidar mutuwa kafin kona gawar dan uwan su

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Masu zaman makoki sun yi matukar kaduwa yayin da wata mata da ake tunanin ta mutu ta farka a cikin tashin hankali kafin a kai ga kona ta.

Bujji Aamma mai shekaru 52 daga Berhampur, Indiya, ta kone sosai a wata gobarar gida a ranar 1 ga Fabrairu kuma an shirya kona ta bayan an ayyana cewa ta mutu.

Kara karanta wannan

Mijina yana min sata don ya siya kwayoyi, Matar aure mai neman saki a kotu

Matar da mijinta ya ayyana ta mutu ta buɗe ido ana dab da kona ta.
Matar da mijinta ya ayyana ta mutu ta buɗe ido ana dab da kona ta.
Asali: Getty Images

Bayan gobarar, an kai ta asibitin kwalejin kiwon lafiya na MKCG don yi mata magani, amma aka koma da ita gida, sabone munin da abin ya yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

The Mirror ta rahoto cewa ba samu ci gaba da jinyar ta ba saboda rashin kudi na iyalin, wannan ne ma ta sa suka kasa kai ta wani asibitin.

Sibaram Palo ya ayyana matarsa Aamma ta mutu

Bayan ƴan kwanaki, ranar litinin, bata buɗe idonta ba kuma babu alamar wani motsi a jikinta, daga nan mijinta ya ayyana ta mutu.

Mijin Aamma, Sibaram Palo don haka ya shirya a kai ta wurin da ake gona gawa a cikin motar daukar gawa.

Ya gaya wa Times of India cewa:

"Mun yi tsammanin ta mutu ne kuma muka sanar da wasu mazauna yankin da su shirya motar daukar gawar zuwa wurin kona gawar."

Kara karanta wannan

Gasar AFCON: An shiga karancin rigunan Super Eagles a Kano, 'yan kwasuwa sun kwashi ganima

Abin da Chiranjibi da gidan kona gawar suka ce

Wata mata mai suna K Chiranjibi da ta raka Aamma a cikin motar gawar ta ce sun kusa kammala hada dakin jana’izar ne a lokacin da ta bude ido ga mamakin su.

Chiranjibi ya ce:

"Da farko mun tsorata har wasu na guduwa domin ba mu taba ganin irin wannan lamari ba, duk da cewa mun ji a wasu labarai."

Abin mamaki, a cewar dakin kona gawar, mutanen yankin ba sa bukatar bayar da takardar shaidar mutuwa don gudanar da ibadar karshe na dan uwa, lamarin da ya sa abubuwa kamar haka suka fi faruwa.

AFCON: Mataimakin Bursar na jami'ar Kwara ya rasu

A wani labarin da Legit Hausa ta ruwaito, kun ji yadda mataimakin Bursar na jami'ar Kwara, Alhaji Ayuba Abdullahi ya rasu yana tsaka da kallon wasan Najeriya da Afrika ta Kudu.

Kara karanta wannan

Arziki mai rana: Yadda matashi ya siya abincin mai talla gaba daya, ya rabawa marasa galihu

An ruwaito cewa Abdullahi ya samu hawan jini na take lokacin da aka ba Afrika ta Kudu finareti, wanda ya kai ga wasan ya tashi ci 1-1.

Ko da aka garzaya da Abdullahi asibiti, likitoci sun tabbatar da cewa ya rasu sun kafin a karasa da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.