An sace motar daukan gawa dauke da gawar wata mata

An sace motar daukan gawa dauke da gawar wata mata

- Wani barawo ya yi awon gaba da motar gawa dauke da gawar wata mata a ciki

- An sace motar ne yayin da direbanta ya tsaya a gaba wata Coci domin sauke wata gawar

- Hukumomi sun fitar da jawabi tare da rokon barawon da ya sace motar a kan ya dawo da koda iya gawar matar da ke cikin motar ne

Hukumomi a jihar Los Angeles, kasar Amurka, sun fara gudanar da bincike a kan yadda aka sace wata motar daukan gawa da aka sace dauke da gawar wata mata a ciki.

An sace Motar, kirar 'Lincoln Navigator ' mai bakin fenti, a gaban Cocin St. Anthony da ke California yayin da direbanta ya tsaya domin sauke wata gawar.

Daily Nation ta rawaito cewa direban motar ya nemi motar ya rasa bayan ya fito daga Cocin St. Anthony, inda ya sauke wata gawa.

A wani rahoto da ABC ta wallafa a ranar da abin ya faru (26 ga watan Fabrairu), hukumomi sun roki barawon motar ya daure ya dawo da gawar matar da ke cikin motar idan ma ba zai dawo da motar ba.

"Haba! Duk da cewa barawo ya saba aikata laifi, ya kamata wannan barawo ya yi abin kirki sau daya a rayuwarsa; ya dawo da gawar da ke cikin akwatin gawa a cikin motar," a wata sanarwa da jami'in dan sandan ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Tuwita.

DUBA WANNAN: Hotunan haduwar biloniyoyi; Aliko Dangote ya ziyarci Abdulsamad Isyaka Rabi'u

Sai dai, hukumomin basu bayyana sunan wanda ake zargi da sace motar ko sunan matar da gawarta ke cikin motar ba.

Mahukuntan Cocin sun bayyana cewa sace motar da gawar matar da ke cikin motar da aka sace su da alaka da harkokin Cocin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel