Hassada ta sa Shugaba Babangida ya kashe Vatsa Inji Domkat Bali

Hassada ta sa Shugaba Babangida ya kashe Vatsa Inji Domkat Bali

Janar Domkat Bali wanda ya rike kujerar shugaban sojojin Najeriya a lokacin mulkin sojan Ibrahim Badamis Babangida ya tado da tsohon tarihi game da kisan Janar Mamman Vatsa.

Domkat Bali wanda ya kuma rike Ministan tsaro a sa’ilin da Janar Ibrahim Babangida ya ke mulkin kasar nan ya fito ya bada labari tiryan-tiryan na yadda a kama kama Mamman Vatsa.

A 2006, Babajide Kolade-Otitoju da wasu Abokan aikinsa ‘yan jaridar TheNEWS sun yi hira da Domkat Bali a Ikoyi da ke cikin Legas inda su ka tambayesa ko ya taba yin wani babban kuskure.

Janar Bali ya bada amsa a wancan lokaci da cewa: “Ban sani ba ko akwai. Har yanzu da-na-sanin da na ke yi shi ne ban da tabbacin ya dace a ce mun kashe kashe Janar Mamman Vatsa.”

Domin ba mu tara wasu hujjoji masu karfi da ke nuna cewa ya cancanci kisan-kai ba. Da na-sanin kurum da na ke yi shi ne da na gaza cewa ba zan iya kashe shi ba Inji tsohon Sojan.

Tsohon shugaban sojan na Najeriya shi ne ya sanar da laifin da a ke zargin Mamman Vatsa da shi na kifar da gwamnatin Soja wanda har hakan ya kai ga rasa ransa a farkon Watan Maris na 1986.

KU KARANTA: Duniya ba ta taba ganin Barawo irin Sani Abacha ba - Omokri

A Agustan 2019, lokacin da tsohon shugaban kasa Babangida ya cika 78, wata jarida ta kakkabe wannan hira da a ka yi da babban jami’in soja da ya ke ganin gwamnatin IBB ta yi kuskure.

Tsohon sojan ya ce: “Ban da tabbacin mun yi daidai wajen kashe shi (Vatsa).” Da a ka shake shi da tambaya sai Bali ya ce” Babu matsala, ba shi kadai a ka cafke ba, an kama wasu a lokacin.

Akwai wadanda su da aka kama da laifi a lokacin wanda a matsayi na, na shugaban hafsun sojoji (wanda ke kula da duka jami’an kasa da na sama da na ruwa), ni ne mai bada sanarwar, Inji Bali.

Bali ya ce, mun kashe wadanda a ka samu da laifi kafin mu fito mu fadawa Duniya. Na kan tambayi kai na ko me ke damu na a lokacin da na bada wannan sanarwa bayan an riga cika aiki.

A cikakkiyar hirar da a ka yi a wancan lokaci, Domkat Bali ya nuna hassada ce ta sa Babangida ya kashe Aminin na sa. Mamman Vatsa ya kasance babban Abokin IBB tun su na kananan yara.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel