Bama-Bamai Sun Kashe Mutane Fiye da 100 a Wajen Makokin Janar Qasem Soleimani
- Ana da tabbacin mutum sama da 100 sun sheka barzahu a wani hari da ake tunani aikin wasu ‘yan ta’adda ne
- Masoyan Marigayi Qasem Soleimani sun taru domin tunawa da shi, sai bama-bamai su ka fashe a Kerman
- Hukumomin jihar Kerman a kasar Iran sun ce adadin wadanda su ka rasu sun haura 100 kuma wasu na asibiti
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Iran - Akalla mutane 103 aka samu labarin sun mutu a kasar Iran a ranar Laraba a sakamakon wasu bama-bamai da su ka fashe.
Rahotanni daga tashar talabijin Iran a ranar Laraba sun kira lamarin da harin ‘yan ta’adda da aka kai yayin tunawa da Qasem Soleimani.
Makokin Janar Qasem Soleimani a Iran
Shekara hudu kenan da aka hallaka Janar Qasem Soleimani, a dalilin haka wasu su ka taru domin tunawa da tsohon gwarzon sojan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
The New York Times ta ce bama-baman sun tashi ne a kusa da masallacin Saheb al-Zaman da ke Kerman watau mahaifar Soleimani.
Wasu masoya sun maida shi a al’ada, a lokaci irin wannan da aka birne tsohon sojan, su kan kai ziyara domin a tuna da tsohon Janar din.
..Bayan an yi wa Hamas illa
Wannan mummunan lamari ya faru ne ‘yan kwanaki kadan bayan an tabbatar da mutuwar jagoran Hamas, Saleh al-Aruri a Lebanon.
Saleh al-Aruri yana da kyakkyawar alaka da kasar Iran inda bama-baman su ka yi barna.
Su wanene su ka kashe mutane a Iran?
Mataimakin gwamnan jihar Kerman, Rahman Jalali ya ce ‘yan ta’adda su ka kai harin na jiya.
Zuwa yanzu babu wani ko wata kungiya da ta dauki nauyin harin. Abin da aka sani shi ne hukumar IRNA ta ce an rasa mutane har 103.
Da farko an kawo rahoto cewa mutane 73 su ka mutu, daga baya adadin ya yi ta karuwa kamar yadda tashar CNN ta fitar da labarin.
Baya ga haka, IRNA ta ce akwai mutane 141 d su ka samu rauni, daga cikinsu akwai wadanda su ke cikin mawuyacin hali, rai ga Allah.
Kisan Qaseem Soleimani a 2020
An birne Soleimani a birnin Kerman a kusa da filin jirgin Baghdad a kudancin kasar Iran, ana zargin akwai hannun Donald Trump a kisan.
A dalilin haka wasu su ka sa kudi masu yawa har fam Dala miliyan 80 ga wanda ya kawo kan shugaban Amurkan a lokacin a kasar Iran.
Asali: Legit.ng