Jirgin Saman Isra’ila Ya Kashe Mataimakin Shugaban Dakarun Hamas a Lebanon

Jirgin Saman Isra’ila Ya Kashe Mataimakin Shugaban Dakarun Hamas a Lebanon

  • Kasar Lebanon ta bayyana rashin jin dadi da yadda Isra’ila ta kai hari cikinta ba tare da wata gayya da ke tsakani ba
  • An kashe daya daga cikin na hannun daman shugaban kungiyar Hamas da ke yaki da Isra’ila na tsawon lokaci
  • Rahotanni a baya sun bayyana yadda Isra’ila ke yiwa jama’ar Gaza kisan kiyashi ba tare da la’akari da mata da yara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

Beirut, Lebanon - A wani hari da Isra’ila ta kai kan mazauna Beirut ta kasar Lebanon, ta yi ikrarin cewa, hari ne kan daya daga cikin shugabannin kungiyar hamayyarta Hamas, BBC News ta ruwaito.

Mark Reveg, mai magana da yawun Isra’ila ya ce, mataimakin shugaban Hamas, Saleh Al-Arouri ya mutu a wani harin da jirgin Isra’ila ya kai kan shugabannin Hamas.

Kara karanta wannan

Mataimakin shugaban majalisar dattawa ya raba motoci 60 a jihar Kano, ya faɗi muhimmin dalili 1

Kungiyar Hamas dai ta yi Allah-wadai da wannan kisa na shugabanta, inda kawarta kai harin ma tun da fari wani yunkuri ne na takalar rikici a Lebanon.

An kashe mataimakin shugaban Hamas
Yadda Isra'ila ta kashe mataimakin shugaban Hamas | Hoto: @abcnews, FRANCE24
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lebanon ta ce Isra’ila na takalar fada

Firayinministan Lebanon ya zargi Isra’ila da tunzura kasar tare da kokarin janyo ta cikin yakin da ake fafatawa, rahoton Reuters.

Kafafen yada labarai a Lebanon sun ruwaito cewa, an kashe shugaban na Hamas ne a wani harin jirgi mai sarrafa kansa a Kudancin Beirut tare da wasu mutane shida da ke alaka da Hamas.

Shugaban da aka kashe ya kasance babban jigo a tawagar Qassam ta Hamas mai kula da bangaren makamai kuma na kusa shugaban kungiyar Ismail Haniyeh.

Meye ya kai shugaban Hamas Lebanon?

Ya kasance ne a Lebanon a matsayin wakilin hadaka tsakanin Hamas da Hezbullah.

Wannan dai wani babban lamari ne da ya faru tun bayan da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare kan mazauna Gaza da sunan daukar fansa, inda suka kashe yara da mata ba adadi.

Kara karanta wannan

Bayan ya samu babbar matsala, gwamnan PDP ya yi magana kan hakura da mukaminsa

Ya zuwa yanzu, wasu kasashen duniya na ci gaba da tofin Allah-tsine ga yadda Isra’ila ke saba dokar hakkin dan Adam.

Adadin mutanen da Isra’ila ta kashe a Gaza

A wani labarin, gwamnatin Hamas ta ce ya zuwa yau Lahadi adadin mutanen da suka mutu sakamakon fadan da ake gwabzawa tsakanin sojojin Isra'ila da mayakan Hamas a yankin Falasdinu ya kai 13,000.

Rikici tsakanin Isra'ila da Hamas ya fara ne tun ranar 7 ga watan Oktoba., inda mayakan Hamas suka farmaki mazauna Isra'ila, Channels Tv ta ruwaito.

Bayan haka ne gwamnatin Isra'ila ta fara kai harin daukar fansa kan mazauna Gaza a nufin lallasa dakarun Hamas da ke boye a ramukan kariya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel