Yadda Trump ya yanke shawarar kashe Soleimani

Yadda Trump ya yanke shawarar kashe Soleimani

A lokacin da tawagar tsaro na kasa na shugaba Trump suka tafi gidan hutawarsa na Mar-a-Lago da ke Florida a ranar Litinin, ba suyi tsamanin zai amince da shirin zuwa kashe Janar Qassem Soleimani ba.

Sakataren gwamnati Mike Pompeo, Sakataren Tsaro Mark Esper da Janar Mark Milley, shugaban kwamitin shugabanin hukumomin tsaro sun tafi Palm Beach, Florida don sanar da Trump hare-haren saman da Amurka ta kai a Iraqi da Syria a kan masu tayar da kayan baya na Iran da 'yan Shi'a ke marawa baya.

A cikin bayanan tsaron da aka nuna wa Trump, a karshe an jero matakan da Amurka za ta iya dauka ciki har da kashe Soleimani, shugaban rundunar tsaro ta musamman na Quds a cewar wani sanatan Amurka da jami'an da suka hallarci taron amma ba a basu izinin magana a hukumance ba kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

DUBA WANNAN: An kori wata musulma daga wurin aiki saboda ta saka hijabi

Kwatsam, Trump sai ya zabi cewa a kashe Soleimani inji jami'in, ya kara da cewa wasu daga cikin masu bawa shugaban na Amurka shawara sun goyi bayan wannan zabin nasa.

Hakan na nuna cewa nauyi ya rataya a kan Pentagon da zartar da umurnin na shugaban kasa Trump.

Sai bayan taron da Trump ne mahukunta a kasar suka fahimci cewa akwai yiwuwar Amurka za ta sake daukan mataki bayan harin farko da ta kai.

Esper ya shaidawa manema labarai cewa, "A tattaunawar da muka yi da shugaban kasa a yau, mun bayyana masa sauran zabin da muke da shi.

"Na lura cewa zamu dauki wasu matakai idan akwai bukatar hakan."

Ba a bayyana sunan Soleimani a fili ba a matsayin wanda ake son a kashe.

Hukumomin tattara bayanan sirri na Amurka da suka dade suna tattara bayanai a kan Soleimani sun san cewa zai yi tafiya zuwa Lebanon da Syria.

Sun gano cewa zai shiga jirgi daga Damascus zuwa Baghdad cikin 'yan kwanaki.

Jami'an sun ce bisa ga dukkan alamu bai damu ya sirrinta tafiyar ta shi ba.

Jami'an Iran sun ce zai tasi da Syria ne zuwa Baghdad a cikin jirgi da ba na sirri ba domin ya gana da wasu jami'an gwamnatin Iraqi.

Sai dai jami'an gwamnatin Amurka sunyi ikirarin cewa akwai wata makirci da zai tafi shiryawa a tafiye-tafiyensa. Sun ce yana kan shirya wani mummunan hari ne da za a kaiwa gine-ginen Amurka da ke kasashen Gabas ta tsakiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel