Qasem Soleimani: Ana rade-radin za a biya duk wanda ya kawo kan Donald Trump $80m a Iran

Qasem Soleimani: Ana rade-radin za a biya duk wanda ya kawo kan Donald Trump $80m a Iran

Mun samu labari cewa a sakamakon rikicin Iran, an sa kudi ga duk wanda ya iya kawo kan shugaban kasar Amurka, Donald Trump.

Wani daga cikin wadanda su ka shirya sallar jana’izar Janar Qasem Soleimani a kasar Iran, ya na neman yadda za a biya kudi da kan Trump.

Wannan Mutumi ya yi kira ga ‘Yan kasar su bada gudumuwa domin a biya miliyoyin kudi ga wanda ya iya kawo kan shugaban Amurkan.

Kamar yadda mu ka samu labari daga Jaridun kasar waje, an bukaci kowane mutumin Iran ya bada Dala 1 rak har a tara Dala miliyan 80.

Wani gidan talabijin na kasar Iran ya bada wannan sanarwa kwanan nan, bayan Donald Trump na kasa Amurka ya sa an kashe Sojan kasar.

KU KARANTA: Wasu tsofaffin Fastoci sun zama Musulmai a Kudancin Najeriya

Qasem Soleimani: Ana rade-radin za a biya duk wanda ya kawo kan Donald Trump $80m a Iran
Donald Trump ya tsokano Iran bayan ya kashe Qasem Soleimani
Asali: UGC

Wannan kudi euro fam miliyan £60 da ake neman Iranawan su tara, sun kai kusan Naira biliyan 28 idan aka yi lissafi a kudin kasar Najeriya.

George Lopez shi ne ya fara yada wannan labari a shafinsa na Instagram, wanda wannan ya jefa sa cikin matsala har aka soma kiran a kama shi.

Lopez ya yi ikirarin cewa Mutanen kasar Iran sun bada sanarwar ganima da kan Trump ne a lokacin da ake yi wa Marigayi Soleimani sallar gawa.

Kafin mutuwarsa, Janar Qasem Soleimani, babban Soja ne da Iran ta ke ji da shi. A kwanakin baya shugaban Amurka ya sa aka harbe wannan Soja.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel