Jerin Kasashen Duniya Da Sarakuna Ke Mulkarsu Ya Zuwa Yanzu
Yayin da zamani ya kawar da tsarin mulkin gargajiya, akwai kasashe da dama har yanzu da ke amfani da tsarin.
Mulkin gargajiya wani tsari ne na mulki da sarakuna ke jagorantar yanki ko kasa tare da karfin iko kan wadanda ake jagoranta.
A lokacin da dimukradiyya da tsarin kundin tsarin mulki ke zama ruwan dare, wasu kasashe na rungumar tsarin inda maganar sarakunan ke zama doka.
Har yanzu wasu kasashe na amfani da tsohon tsarin na mulkin sarakuna a kasashensu.
Legit ta tattaro muku jerin kasashen da su ke amfani da tsohon tsarin ya zuwa yanzu:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Brunei
Kasa ce da ke yankin tsibirin Borneo da ke Kudu maso Gabashin Nahiyar Asia.
Sultan Hassanal Bolkiah shi ke mulkin kasar tun 1967 wanda shi ne ke da ikon sauya dokoki a kasar kuma shi ne shugaban gwamnatin da kuma siyasar kasar.
Brunei na amfani da shari'ar Musulunci a matsayin hanyar samar da doka a kasar.
2. Oman
Kasar na yankin Larabawa wacce aka fi sani da 'Sultanate of Oman' wanda iyalan Al Said ke jagorantar kasar.
Sultan Haitham bin Tariq Al Said shi ke jagorantar kasar tun a 2020 inda ya gaji Qaboos bin Said wanda ya mulki kasar na tsawon shekaru 50.
3. Qatar
Kasar na bin tsarin mulki na sarauta wanda Sarkin kasar ke jagorantar bangaren gwamnati da na siyasa.
Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani shi ke jagorantar kasar tun 2013 inda iyalan gidansu ke mulki tun tsakiyar karni na 19.
4. Daular Kasashen Larabawa (UAE)
Wannar kasa ta kunshi yankuna bakwai wanda sarki daya ke jagorantarsu a matsayin shugaba.
Wadannan yankuna da ke UAE sun hada da Abu Dhabi da Dubai da Sharjah da Ajman.
Sauran sun hada da Umm Al-Quwain da Ras Al Khaimah da Fujairah yayin da Abu Dhabi ta kasance babban birnin dukkan kasashen.
5. Saudiyya
Kasar Saudiyya na amfani da tsarin mulkin sarakuna wanda sarki ke da karfin iko kan komai da ya shafi siyasa da mukamai.
Karkashin Sarki akwai majalisar ministoci da su ke taimakawa sarki wurin tsare-tsare na gwamnati.
Tinubu Ya Cin Ma Nasarori 3 Bayan Ganawa da Shugaban UAE
A wani labarin, Shugaba Bola Tinubu ya samu nasarar kawo karshen takunkumin da aka kakabawa Najeriya a UAE.
Tinubu da shugaban UAE, Mohamed bin Zayed Al Nahyan ne su ka cin ma wannan matsaya a zaman da su ka yi a ranar Talata 12 ga watan Satumba.
Asali: Legit.ng