Hukumar Saudiyya ta umarci kasashe su dakatar da karbar kudin aikin Hajjin bana

Hukumar Saudiyya ta umarci kasashe su dakatar da karbar kudin aikin Hajjin bana

Hukumar kasar Saudiyya ta umarci kasashen duniya su dakatar a karbar kudin maniyyata aikin Hajjjin bana da ake saka ran gudanar wa a cikin shekarar nan.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanar wa da ma'aikatar aikin Hajji da Umrah ta kasar Saudi Arabia ta fitar a ranar Talata, 31 ga watan Maris.

A cikin sanarwar da ministan ma'aikatar ya wallafa a shafinsa na Tuwita, ya ce za a dakatar da karbar kudin maniyyatan ne har zuwa lokacin da al'amura za su koma daidai.

A cewar sanarwar, ba za a yi gaggawar yanke hukunci a kan aikin Hajjin bana ba har sai an ga yadda abubuwa zasu je su dawo dangane da barkewar annobar cutar coronavirus a fadin duniya.

Sanarwar ta bayyana cewa hukumar kasar Saudiyya ta mayarwa da duk wanda ya biya bizar Umrah kudadensu.

Dangane da wadanda dokar hana shige da fice ta ritsa da su a cikin kasar, sanarwar ta ce za a basu matsuguni a Otal na alfarma tare da basu kulawa ta musamman har zuwa lokacin da za a mayar da su kasashensu.

A kan barin wasu tsirarun mutane su gudanar da dawafi, Saudiyya ta ce ta dauki matakin ne a matsayin rigakafi.

DUBA WANNAN: Annobar coronavirus: An gurfanar da wani limami da wadanda ya jagoranta sallah a Kaduna

A ranar Lahadi ne hukumar kasar Saudi Arabia ta sanar da cewa wasu mutane 66 da suka kamu da kwayar cutar coronavirus sun warke.

Sanarwar na kunshe ne a cikin sakon da babbar jaridar kasar Saudiyya da ake wallafa wa cikin harshen turanci; 'Saudi Gazette' ta fitar ranar Lahadi.

Akwai kimanin mutum 96 da aka tabbatar da cewa sun kamu da kwayar cutar coronavirus a kasar Saudiyya tare da asarar rayukan mutane 8.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel