Isra’ila Ta Kashe Falasdinawa 198 Yayin Harin Ramuwar Gayya Ga Hamas

Isra’ila Ta Kashe Falasdinawa 198 Yayin Harin Ramuwar Gayya Ga Hamas

  • Sojojin Isra'ila sun kai farmaki kan Gaza bayan kungiyar Hamas ta harba makaman roka kan Isra'ila
  • Ma'aikatar lafiya ta Falasdinawa ta sanar da cewa mutane 198 sun mutu yayin da fiye da 1,600 su ka ji rauni
  • Isra'ila na kai manyan hare-hare kan Falasdinawa bayan harin da Hamas ta kai musu da makaman roka

Hamas, Isra'ila - Jami'an lafiya a Gaza sun tabbatar da cewa mutane 198 Falasdinawa sun rasa ransu yayin harin Isra'ila.

Wannan na zuwa ne bayan Hamas ta kai farmaki kan Isra'ila da ya yi sanadin mutuwar mutane 40.

Isra'ila ta kai farmakin ramuwar gayya kan Hamas
Isra’ila Ta Kashe Falasdinawa 198 Yayin Wani Hari. Hoto: Mahmud HAMS/AFP.
Asali: Getty Images

Yaushe Hamas ta kai harin kan Isra'ila?

Aljazeera ta tattaro cewa fiye da mutane 1,600 su samu raunuka yayin harin na yau Asabar 7 ga watan Oktoba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Shehu Sani Ya Yi Martani Kan Zargin Satar Mazakuta A Abuja, Ya Ba Da Shawara

Tun farko kasar Isra'ila ta sanar cewa ta fara kai farmaki a yankin Gaza bayan Falasdinawa sun addabe su da hare-hare.

Rikicin ya fara ne bayan Hamas ta kai hari kan Isra'ila kan abun da ta kira kai hare-hare ba kakkautawa kan masallacin Qudus.

Yadda Hamas ta kai hari kan Isra'ila

Har ila yau, bayan Hamas ta harba dubban makaman roka kan Isra'ila, Falasdinawa masu dauke da makamai sun shiga kasar ta ruwa da kuma ta kasa don kara far musu 'yar ba zata.

Fada mai tsanani ya barke tsakanin sojojin kasashen guda biyu inda ake zargin Hamas na rike da 'yan Isra'ila a garin Gaza, cewar CBS News.

An jiyo motocin jami'an tsaro ma su gargadi na ta kai-kawo a biranen Tel Aviv da Jarusalam da sauran birane da ke kasar Isra'ila.

Hamas ta Falasdinawa ta kai mummunan hari kan Isra'ila

A wani labarin, Kungiyar Hamas da ke kare Falsdinawa ta kai wani hari kan Isra'ila inda mutane da dama su ka rasa rayukansu.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar Da Shirin N-Power, Ta Bayyana Dalilai Masu Zafi

Hamas ta kai hare-haren ne a yau wanda ake ganin na daga hari mafi muni tun shekarar 2021 a kan Isra'ila.

Fada tsakanin Falasdinawa da Isra'ila tun ba yau aka fara akalla sun shafe shekaru su na gwabzawa a yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.