Juyin Mulkin Nijar: Sarkin Musulmi Ya Yi Watsi Da Takunkumin ECOWAS Da Tsoma Bakin Sojoji

Juyin Mulkin Nijar: Sarkin Musulmi Ya Yi Watsi Da Takunkumin ECOWAS Da Tsoma Bakin Sojoji

  • Akwai sabon ci gaba dangane da tukunkumi ECOWAS da tsoma bakin sojoji a Jamhuriyar Nijar
  • Majalisar Koli ta harkokin Musulunci a Najeriya karkashin jagorancin Muhammad Abubakar ta yi adawa da takunkumin ECOWAS da yunkurin sojoji kan masu juyin mulki a Nijar
  • Majalisar ta bukaci kungiyar ECOWAS da Tinubu ke jagoranta, da ta yi amfani da sulhu ba dole ba wajen tattaunawarta da shugabannin juyin mulki

Jihar Sokoto - Majalisar Koli ta harkokin Musulunci a Najeriya (NSCIA) ta bayyana matsayinta dangane da takunkumin da kungiyar kasashen yammacin Afrika (ECOWAS) ta kakaba ma jamhuriyar Nijar.

Majalisar Musuluncin ta yi adawa da takunkumin kungiyar EWCOWAS a kan shugabannin juyin mulkin Nijar

Sarkin Musulmi ya aika sako ga Tinubu kan juyin mulkin Nijar
Juyin Mulkin Nijar: Sarkin Musulmi Ya Yi Watsi Da Takunkumin ECOWAS Da Tsoma Bakin Sojoji Hoto: @Abdulfagge
Asali: Twitter

Dalilin da yasa Majalisar Musulunci ta yi watsi da takunkumin ECOWAS ta kakaba wa gwamnatin mulkin Soja

A ranar Laraba, 9 ga watan Agusta, mataimakin babban sakataren NSCIA, Salisu Shehu, ya ce majalisar ta yi adawa da takunkumin da ECOWAS ta kakabawa Nijar sakamakon juyin mulkin da aka yi a ranar 26 ga watan Yuli a kasar ta yammacin Afrika, rahoton Premium Times.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Tinubu Da Wasu Shugabanni 7 Sun Fara Taron ECOWAS Kan Juyin Mulkin Nijar

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NSCIA ta ce:

"An sani sarai cewa irin wannan takunkumin na tattalin arziki ba sa da amfani kuma a karshe suna karewa a banza."

Sarkin Musulmi ya aika sako ga Shugaban kasa Tinubu

Majalisar NSCIA, karkashin jagorancin sarkin Musulmi, Muhammad Abubakar, ta kuma bayyana rashin amincewarta da amfani da karfi wajen fatattakar shugabannin sojojin da suka hambarar da shugaba Mohamed Bazoum daga mukaminsa a watan jiya.

A halin da ake ciki, ECOWAS a baya ta kakabawa Nijar takunkumi bayan juyin mulkin. Takunkumin ya hada da rufe iyakokin sama da na kasa, daskarar da asusun Nijar a bankunan tsakiya na ECOWAS, da dai sauransu, rahoton Daily Trust.

"Ka yi amfani da tattaunawa ba karfi ba", Sultan ya fadawa Tinubu

A cikin sanarwarta, majalisar NSCIA ta amince cewa masu juyin mulkin sun bijire wa matsayarsu, amma ta bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda shi ne shugaban kungiyar ECOWAS, da ya nemi sulhu yayin tunkarar gwamnatin mulkin soja.

Kara karanta wannan

Sojojin Nijar Sun Aikawar Da Wata Sabuwar Doka A Kasar, Janar Tchiani Ya Yi Bayani

A halin yanzu, NSCIA ita ce kungiyar Musulunci mafi karfi a Najeriya inda miliyoyin Musulmai ke daukar Sultan a matsayin shugabansu.

Juyin mulki: Sanusi ya gana da Tinubu bayan ya dawo daga Nijar

A wani labarin kuma, mun ji cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da mai martaba Sarkin Kano na 14, Sanusi Lamido Sanusi suna cikin wata ganawa ta sirri yanzu haka a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

A baya-bayan nan ne Sanusi ya dawo daga Jamhuriyar Nijar inda ya je ganawa da shugabannin juyin mulki wadanda suka kwace mulki daga hannun zababben shugaban kasa Muhamed Bazoum.

Asali: Legit.ng

Online view pixel