Matar Da Ta Haifi Yara 44 Ta Ce Tana Son Kari, Likitoci Sun Kasa Juya Mahaifarta

Matar Da Ta Haifi Yara 44 Ta Ce Tana Son Kari, Likitoci Sun Kasa Juya Mahaifarta

  • Mariam Nabatanzi ta kafa tarihi ta hanyar haihuwar yara har guda 44 kuma ita kadai ke kula da su
  • Ta haifi danta na fari tana da shekaru 13 a duniya, kuma a lokacin da ta yi haihuwa na biyu, yaranta sun kai su bakwai
  • Mariam wacce aka yiwa lakabi da uwar Uganda ta haifi yan hudu-hudu sau biyar
  • Yanzu shekarunta 41 a duniya kuma ta ce tana da burin sake haihuwar wasu yaran amma da mijin da ya dace

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wata mata a kasar Uganda ta hau kanen labarai kan samun abun da ba dukka mata ke mallaka ba, musamman a shekarunta.

Mariam Nabatanzi ta kasance mace mai shekaru 41 a duniya wacce ke da yara 44 a gabanta kuma ita kadai ke kula da su. Uwar Uganda ko uwar Afrika kamar yadda ake kiranta, Natabanzi ta bayyana cewa ba za ta daina haihuwar ‘ya’ya ba.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Dumi: 'Yan bindiga sun kai kazamin hari kan matafiya a Katsina, sun kashe rayuka

Uwa da 'ya'yanta
Matar da ta haifi yara 44 ta ce tana son kari, likitoci sun kasa juya mahaifarta Hoto: Afrimax English.
Asali: UGC

Haihuwar yan hudu da yan biyu

Nabatanzi ta ce ta haifi dukka yaranta ne a yayin soyayya da wani mutum, wanda ya yi watsi da ita, kamar yadda Afrimax English ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta haifi danta na fari tana da shekaru 13 a duniya bayan iyayenta sun siyar da ita ga wani tsoho mai shekaru 57 a duniya.

“Na haihu sau 15. Na haifi yan hudu sau biyar. Da tagwayena za su zama shida amma seti daya dun mutu, don haka shima ya zama sau biyar kenan,” in ji ta.

Yara bakwai kacal ta so

Duk da auren dole aka yi mata tana da shekaru 12, Mariam bata yanke kauna da fadawa soyayya ko samun karin yara ba.

“Idan na samu damar haduwa da mutum nagari, zan haifo karin yara saboda haihuwa ba aibu bane. Haihuwa kyauta ce daga Allah,” in ji ta.

Kara karanta wannan

Budurwa ta kai saurayi kotu kan ya ki zuwa wurin shakawatar da suka yi za su hadu, tana bukatar diyyar N4m

Da take tasowa, Nabatanzi bata san ya rayuwa za ta kasance gare ta ba, amma ta san yara nawa take so.

“Yara bakwai kacal na so haifa,” in ji ta.

Karin yara na nan zuwa

Ta ce yara biyar ta so haifa sannan ta sanya masu sunan yan uwanta da suka mutu, daya sunanta sannan da sunan mijinta.

“Allah ya nufa hakan ya faru, kuma sau biyu kacal, na samu yara bakwai,” cewar Nabatanzi.

Ta je wajen likitoci domin su juya mahaifanta kuma ta yi amfani da dabaru don hana kanta daukar ciki, amma duk a banza.

“Don haka idan na mallaki miji mai fahimta, zan haifi karin ‘ya’ya,” cewar Mariam cike da farin ciki.

Yadda Aka Haifi Jarirai 27,490 Cikin Watanni Uku A Jihar Kano

A wani labari, gwamnatin jihar Kano a ranar Alhamis, 21 ga watan Yuli, ta bayyana cewa an haifi jarirai 27,490 a cibiyoyin kiwon lafiya da ke fadin jihar.

Kara karanta wannan

Mace Yar Shekara 64 Ta Lashe Zaben Shugaban Kasa a Indiya

Babban daraktan hukumar dake kula da asibitoci ta jihar Kano, Nasiru Alhassan, ne ya bayyana hakan yayin da yake kaddamar da shirin rabon kayan kiwon lafiya ga asibitoci a jihar.

A wajen taron, Mista Alhassan, wanda ya samu wakilcin shugaban likitocin gwamnati, Sulaiman Hamza, ya ce daga cikin jariran 27,490 an haifi 681 ta hanyar tiyata, Premium Times ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel