Obasanjo Ya Aika Wasika, Yana Nemawa Sanatan da Aka Samu da Laifi a Ingila Alfarma

Obasanjo Ya Aika Wasika, Yana Nemawa Sanatan da Aka Samu da Laifi a Ingila Alfarma

  • Olusegun Obasanjo ya tsoma baki a shari’ar da ake yi da Ike Ekweremadu da iyalinsa a Ingila
  • Tsohon shugaban Najeriya ya aika wasika zuwa ga Akawun kotun Birtaniya, yana neman alfarma
  • Obasanjo ba komai yake nema ba sai a tausayawa wadanda aka samu da laifi saboda darajar ‘yarsu

Ogun - Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya roki Kotun Birtaniya ta nuna rahama a shari’arda ake yi da Ike Ekweremadu da kuma iyalinsa.

Rahotanni daga The Cable sun tabbatar da cewa Cif Olusegun Obasanjo ya rubuta wasika, yana rokon kotun kasar wajen yayi wa Sanatan Najeriyan afuwa.

Obasanjo wanda ya mulki Najeriya a gwamnatin soja da farar hula, yake cewa Sanata Ekweremadu ya cancanci ayi tir da shi saboda danyen aikin da ya aikata.

Obasanjo ya ce bai kamata ayi wa ‘dan siyasar wani uzuri a kasar da aka cigaba ba, amma duk da haka, dattijon ya ce ya cancanci kotu tayi masa rangwame.

Kara karanta wannan

Mulkin Tinubu: Jiga-jigan 'Yan Siyasa 3 Sun Hada Kai, Sun Fadi Wanda Suke So Ya Zama Shugaban Majalisa

"Ekweremadu mai taimako ne"

A cewar Obasanjo, Sanatan na Yammacin Enugu ya dade yana taimakon marasa karfi tare da matarsa ta karkashin gidauniyarsa, Ikeoha Foundation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasikar da tsohon shugaban na Najeriya ya aikawa Akawun kotun ta roki ayi amfani da ofishinsa wajen neman alfarma Alkalai su sassauta hukunci.

Obasanjo
Olusegun Obasanjo a ketare Hoto : Getty Images
Asali: Getty Images

"Ina so ayi la’akari da alakar da ke tsakanin Birtaniya da gwamnatin tarayya; saboda matsayinsa na zama Sanata Mai girma a majalisar kasar Najeriya
Sannan a duba darajar diyarsu wanda ta ke fama da rashin lafiya a yanzu, sannan ta na bukatar kulawa, ina rokon kayi amfani da ofishinka, ka sa baki.
A nemi gwamnatin Birtaniya tayi rangwame wajen zartar da hukunci, su duba halin kirkinsa da kaunar iyaye wajen zartar da hukunci a kan shi.

Sun ta rahoto Obasanjo yana cewa Ike Ekweremadu da mai dakinsa sun dauki darasi a yanzu.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Bayan PDP, Babbar Kotu Ta Dakatar da Shugaban Jam'iyya Na Ƙasa da Wasu Shugabanni 3

Wasikar ta na kuma kunshe da bayanin kyakkyawar alakar da ke tsakanin shugaban da Sanatan da ke tsare da gudumuwar da ya ba da damukaradiyya.

An samu $800m daga bankin Duniya

A jiya aka ji rahoto Ministar tattalin arziki, Zainab Ahmed ta fadi yadda za su ragewa marasa karfi zafin tashin farashin man fetur a tsakiyar shekarar nan.

Zainab Ahmed ta ce Najeriya ta karbo wasu kudi da sun kai Naira Biliyan 36 daga wajen bankin Duniya domin cire tallafin mai zai jawo wahalar rayuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel