Shugaba Zelensky na Ukraine zai gana da shugaba Xi na China nan ba da jimawa ba
- Shugaban kasar Ukraine, mai girma Zelensky ya ce kasarsa ta shirya karbar bakuncin shugaban kasar China Xi Jinping
- Amurka na bayyana guna-guni kan yunkurin China na sulhunta tsakanin Rasha da Ukraine da ke yaki tun bara
- Ya zuwa yanzu, kasashen biyu sun yi asarar sojoji da fararen hula tun farkon yakin a watan Faburairun bara
Kyiv, Ukraine - Shugaban kasar Ukraine, Volodymyr Zelenskiy ya gayyaci shugaban kasar China, Xi Jinping domin ziyartar kasar da ke Gabashin Turai.
Wannan na fitowa ne daga bakin Zelensky a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a wani taro mai muhimmanci, rahoton CNN.
A cewarsa, kasarsa ta shirya daram domin tarbar shugaban na China, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito.

Asali: UGC
Mun shirya karbar shugaba Xi, inji Zelensky
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan
Jigon PDP Bode George Ya Lissafa Kasashen Da Zai Iya Yin Hijira Saboda Bola Tinubu Ya Zama Zababben Shugaban Kasa
A kalaman Zelensky:
“Mun shirya don ganawa dashi a nan.”
Shugaba Xi na China dai bai taba magana da shugaban Ukraine ba tun bayan da kasar Rasha ta Putin ta kai mummunan farmaki kan mazauna Ukraine a watan Faburairun bara.
Sai dai, a watan da ya gabata ne China ta fitar da wasu manufofi 12 na yadda za a warware matsalolin da ke tsakanin Rasha da Ukraine, UkrinForm ta tattaro.
Xi ya tattauna kan batun rikicin da abokinsa na kut-da-kut, wato shugaban Rasha Vladimir Putin a lokacin da ya ziyarci birnin Moscow ta Rasha a makon jiya.
Sai dai, tattaunawar shugabannin biyu bata bayyana hanya kai tsaye na yadda za a kawo karshen yakin kasashen na Rasha da Ukraine ba.
Kadan daga abin da China ta yi kira akai shine, duba yiwuwar tsakaita wuta a yakin da aka kai kan kasar ta Ukraine.
Amurka na guna-guni kan yunkurin China na sulhunta Rasha da Ukraine
Sai dai, duk da haka kasar Amurka na ci gaba da guna-guni kan yunkurin na China, inda tace shugaba Xi bai taba yin Allah wadai da abin da Rasha ta yiwa Ukraine ba.
A cewar Amurka, janyewar sojojin Rasha da kuma tsakaita wutar zai ba Putin damar ci gaba da nuna iko ga kasashen da ya mamaye da kuma sake hada sojoji masu karfi a nan gaba.
A bangarenta, Ukraine dai ta yi na’am da shiga tsakani na diflomasiyya da China za ta yi, amma Zelensky ya ce za a janye yankin ne kawai bayan sojojin Rasha sun tattara sun fice daga lardin Ukraine.
A baya, Zelensky ya bayyana kukan cewa, kasar Rasha na kokarin rusa masa kasa tare da hallaka al’ummar da yake mulka.
Asali: Legit.ng