Jigon PDP Bode George Ya Lissafa Kasashen Da Zai Iya Yin Hijira Saboda Tinubu Ya Zama Zababben Shugaban Kasa

Jigon PDP Bode George Ya Lissafa Kasashen Da Zai Iya Yin Hijira Saboda Tinubu Ya Zama Zababben Shugaban Kasa

  • Jigon Peoples Democrtic Party, PDP, kuma jagora a Jihar Lagos, Bode George ya fayyace abin da ya ke nufi kan alkawarin da ya dauka na barin Najeriya idan Bola Tinubu na jam'iyyar APC ya lashe zaben 2023
  • A wata tattaunawa da aka yi da shi, George ya ce zai iya zuwa duk kasar da ya ga dama a fasfo dinsa
  • Sai dai, George, ya bayyana cewa zai iya komawa Lome, Cotonou, Iceland da Ghana tare da bayyana cewa bai aikata wani laifi da zai hana shi yawo ba

Tsohon shugaban jam'iyyar Peoples Democrtic Party, PDP, na kasa, Cif Olabode George ya sake magana kan shirinsa na barin Najeriya bisa ra'ayin kansa.

Jigon na Peoples Democrtic Party, PDP, a ranar Litinin, 27 ga watan Maris, ya ce hakkinsa ne ya zabi inda ya ke son zama a fadin duniyar nan.

Kara karanta wannan

"An Hada-Kai da INEC, Za a Murde Zaben Gwamna a Jihar Adamawa" Inji Jam’iyyar PDP

Bola and Bode
Jigon PDP Bode George Ya Bayyana Jerin Kasashen Da Zai Tafi Hijarar Dole Saboda Tinubu Ya Zama Shugaban Kasa
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bode George ya yi magana kan yin hijira bayan nasarar Tinubu, kasashen da ya yanke shawarar zuwa

George, wanda ya magana a shirin gidan talabijin na Channels, Politics Today ranar Litinin, ya ce zai komawa kasashen da ke makwabtan Najeriya a Afirka ta Yamma kamar Ghana, Cotonou a jamhuriyyar Benin da Lome a Togo idan bai gamsu da salon mulkin shugaba mai jiran gado ba, Bola Tinubu.

Da aka tambaye shi ranar Litinin ko ya na tunanin gudun hijira, George ya ce,

''Ban boye ra'ayi na ba: Na ce idan wannan mutumin (Tinubu) ya zama shugaban kasa, zan daina ra'ayin siyasa.''

Karanta abin da ya ce a kasa don tabbatar da matsayarsa;

''Ban aikata wani laifi da zai iya dakatar da ni ba. Zan iya komawa Lome in rayu. Zan iya zuwa Cotonou. Zan iya zuwa Ghana. Zan ma iya zuwa Iceland. Zan iya zuwa duk inda na ke so. Da fasfo dina da cancanta ta da mutunci na, zan iya rayuwa ko ina. Kawai na damu ne da rayuwar yan baya.''

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Rikici Ya Tsananta, Gwamna Wike Ya Maida Martani Mai Zafi Kan Dakatar da Shugaban PDP

Ban janye wa wani takara ba, in ji dan takarar gwamnan LP na Kaduna, Asake

A wani rahoton daban, dan takarar gwamna na jam'iyyar LP a Jihar Kaduna ya yi watsi jita-jitar cewa ya janye wa, Isah Ashiru, dan takarar jam'iyyar People Democratic Party, PDP, gabanin zaben ranar Asabar da ke tafe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel