Watanni 3 Kafin Ya Bar Mulki, Kasashen Afrika Za Su Karrama Shugaba Buhari

Watanni 3 Kafin Ya Bar Mulki, Kasashen Afrika Za Su Karrama Shugaba Buhari

  • ECOWAS za ta karrama Muhammadu Buhari a dalilin kokarin da ya yi wa yammacin Afrika
  • Kungiyar ta ce Shugaban Najeriya ya taka rawar gani wajen tabbatar da tsarin damukaradiyya
  • Malam Garba Shehu ya fitar da jawabi, ya ce Shugaban ECOWAS ya yaba da kokarin mai gidansa

Qatar - Kungiyar ECOWAS ta kasashen yammacin Afrika ta ce za ta karrama Muhammadu Buhari saboda kokarin da ya yi a kan mulki.

Jaridar The Cable ta ce Garba Shehu ya bada sanarwar cewa ECOWAS za ta ba shugaban Najeriyan lambar yabo a dalilin cigaban da ya kawo.

Garba Shehu ya fitar da jawabi a ranar Talata yana cewa Shugaban kungiyar kasashen yankin, Umaro Sissoco Embalo ya shaida wannan.

Shugaban Bissau-Guinea, Umaro Sissoco Embalo ya yi wannan bayani ne a wajen wani zama da ya yi da Buhari a taron majalisar dinkin Duniya.

Taron majalisar dinkin Duniya

Rahoton ya ce shugabannin sun yi zaman ne a kan abin da ya shafi kasashen suke tasowa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da zarar an kammala taron a yau Laraba ake sa ran shugaban na Najeriya zai dawo gida bayan ya shafe ‘yan kwanaki a kasar Larabawan.

Buhari
Shugaba Buhari Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Mai magana da yawun bakin shugaban Najeriyan ya ce kungiyar ECOWAS za ta sa sunan Mai girma Muhammadu Buhari a kundin tarihi.

Shugaba Embalo yake cewa takwaransa na Najeriya ya yi abin da ya fi na kowa a wajen goyon bayan tsarin farar hula a yammacin Afrika.

Embalo ya ce Buhari ya yaki wajen ganin bayan duk wani tsari da ba na farar hula don haka za a rika tunawa da shi a hedikwatar ECOWAS.

Yanzu haka kungiyar kasashen Nahiyar su na gina babban ofishin ECOWAS a babban birnin Abuja. Tribune ta fitar da wannan rahoto dazu.

A bangarensa, Buhari ya yi maraba da wannan karramawa, ya ce a Duniyar yau ta tsarin farar hula ne kurum za a iya kawowa al’umma cigaba.

Mata ba su da wakilci a Majalisa

Mutane 360 ake da su a zauren Majalisar wakilan Najeriya, amma kun samu labari cewa 13 kacal ne mata a cikinsu, kusan kashi 3.33% kenan.

A matan da suka lashe takarar 2023 akwai Zainab Gimba, Fatima Talba, Goodhead Boma, da tsohuwar Minista, Khadija Bukar Abba Ibrahim.

Asali: Legit.ng

Online view pixel