Mata 13 da Za Suyi Kafada da Kafada da Maza a Majalisa Bayan Nasara a Takara

Mata 13 da Za Suyi Kafada da Kafada da Maza a Majalisa Bayan Nasara a Takara

  • Hukumar zabe ta INEC ta fitar da jerin zababbun ‘yan majalisar wakilan tarayya bayan zaben 2023
  • An damkawa wadanda suka yi nasara takardar shaida, nan da kusan watanni uku za su shiga ofis
  • Kashi 3% rak na zababbun ‘yan majalisar tarayyan ne mata, ragowar kusan 97% duka maza ne

Abuja - A wannan kebantaccen rahoto, Legit.ng Hausa ta tattaro maku jerin matan da aka ba takardar nasara, kuma za su zama ‘ya majalisar wakilai.

Ga jerin nan kamar haka:

1. Orogbu Obiageli

Orogbu Obiageli ta lashe zaben majalisar wakilan tarayya na Fubrairu, tana cikin wadanda suka ci kujera a Anambra sanadiyyar guguwar Peter Obi.

2. Nnabuife Chinwe Clara

Kujerar mazabar Orumba a majalisar tarayya ta na hannun Nnabuife Chinwe Clara da tayi nasara a karkashin jam’iyyar YPP, ta doke APC, PDP da su LP.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Ana Saura Kasa Da Kwana 3 Zabe, Shugabar Matan PDP a Sokoto Ta Koma APC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

3. Gwacham Maureen Chinwe

Jam’iyyar APGA ta yi galaba a zaben majalisar tarayya a shiyyar Oyi/Amayelum. Gwacham Chinwe ta na tare da jam'iyya mai mulki a Anambra.

4. Ebikake Marie Enenemiete

A mazabar Brass da ke jihar Bayelsa, jam’iyyar PDP ta samu kujerar majalisar tarayya da kuri’u 11, 415 a zaben bana ta hannun Ebikake Marie Enenemiete.

5. Regina Akume

Tsohuwar uwargidar jihar Benuwai, Regina Akume za ta wakilci mutanen Gboko/Tarka a majalisa bayan nasarar da ta samu a karkashin APC mai-ci.

6. Onuh Onyeche Blessing

Daga cikin kujerun da APC ta samu a Benuwai akwai ta shiyyar Otukpo da Ohimini, hakan yana nufin Onuh Onyeche Blessing za ta zama ‘yar majalisa a 2023.

'Yan Majalisa
Zaman Majalisar Wakilai Hoto: @SpeakerGbaja
Asali: Facebook

7. Zainab Gimba

Hon. Zainab Gimba mai shekara 50 za ta koma majalisa a karkashin APC. ‘Yar siyasar tana wakiltar mutanenta na Bama/Ngala/Kala Balge a birnin Abuja.

Kara karanta wannan

Matsala ta faru: Jerin mazabun sanata 8 da dole za a sake zabe, INEC ta fadi yaushe

8. Ibori – Suenu Erhiateke

A Ethiope, diyar tsohon Gwamnan Delta kuma jigo a PDP, Ibori – Suenu Erhiateke ta doke ‘dan majalisa mai-ci, Hon. Ben Rolands Igbakpa na jam’iyyar NNPP.

9. Onuaho Miriam Odinaka

Onuaho Miriam Odinaka za ta zarce a matsayin ‘yar majalisar Isiala Mbano da kewaye. ‘Yar siyasar da ta fara zuwa majalisa a 2020 ta lashe zabenta a APC.

10. Beni Butmak Lar

A matan da ke majalisar tarayya, Beni Butmak Lar tana cikin wadanda suka fi dadewa a tarihi. Tun a 2007, Lar take wakiltar mazabar Langtang a jam’iyyar PDP.

11. Goodhead Boma

Bayan shafe shekaru hudu a majalisa, Goodhead Boma za ta zarce a kujerar Akuku Toru/Asari Toru a majalisar wakilan tarayya, ‘yar siyasar ta Ribas ‘yar PDP ce.

12. Khadija Bukar Abba Ibrahim

Tsohuwar Ministar tarayya, Khadija Bukar Abba Ibrahim za ta koma majalisa domin wakiltar Damaturu/Gujba/Gulani/Tarmuwa, ‘yar siyasar ta shahara a Yobe.

Kara karanta wannan

INEC ta Bada Dalilin Cire Sunan Yaron Tsohon Gwamna Cikin Zababbun ‘Yan Majalisa

13. Fatima Talba

Mutanen Nangere/Potiskum a jihar Yobe sun sake zaben Hon. Fatima Talba domin ta wakilce su a majalisar tarayya, tayi nasara a kan ‘dan takaran PDP da kuri’u 301.

Mata 2 za su zama Sanatoci

Daga jerin zababbun Sanatoci da aka fitar a makon nan, an samu rahotonmu da ya nuna Ireti Heebah Kingibe da kuma Banigo I. Harry ne kurum mata.

Banigo I. Harry ta yi Kwamishinar ma'aikatar lafiya da SGF kafin zama Mataimakiyar Gwamna, ita Ireti Kingibe ta nemi takara a APC kafin ta ci zabe a LP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng