Gwamna Sule: Na Gama Ta'aziyyar Yara 9 'Yan Gida 1 da Bam ya Kashe, Sai ga Mutuwar Nawa 'Dan

Gwamna Sule: Na Gama Ta'aziyyar Yara 9 'Yan Gida 1 da Bam ya Kashe, Sai ga Mutuwar Nawa 'Dan

  • Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa yace rasuwarsa 'dan hukunci ne na Allah kuma gwajin imani ne gare shi
  • Ya sanar da yadda ya dinga rarrashin wani mai 'ya'ya 9 da suka rasu a bam din da ya tashi sannan ya rasa shanu 70 ana gobe 'dan zai rasu
  • Ya shaida cewa, Allah bai shawarce sa ya bashi Hassan ba, don haka daukarsa ma duk cikin hukuncin Allah ne

Nasarawa - Abdullahi Sule, gwamnan jihar Nasarawa, yace ya duba mutuwar 'dan sa matsayin jarabawa daga Allah, jaridar The Cable ta rahoto.

Hassan Sule
Gwamna Sule: Na Gama Ta'aziyyar Yara 9 'Yan Gida 1 da Bam ya Kashe, Sai ga Mutuwar Nawa 'Dan. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Ya sanar da hakan a ranar Juma'a yayin da yake karbar masu masa ta'aziyya a fadar Sule Bawa, mahaifinsa wanda shi ne Sarkin Gudi na karamar hukumar Akwanga.

Hassan, 'dan gwamnan jihar Nasarawa ya rasu a ranar Alhamis yayin da yake da shekaru 36 a duniya.

Kara karanta wannan

Iko da Rahamar Allah ce Tasa Nake Raye, Na ga Mutuwa a Yakin Basasar Najeriya, Shugaba Buhari

A yayin jawabi ranar Juma'a, Sule yace ya gama rarrahin wani da ya rasa mutum tara a gidansa sakamakon luguden wutan da sojojin sama suka yi a jihar kenan, inda yace ba zai iya tuhumar hukuncin Allah kan mutuwar 'dansa ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Na kalla wannan matsayin jarabawa daga Allah. Ni ne na dinga rarrashin wani da ya rasa yara tara da shanu 70 a jiya, amma yau sai Allah ya yanke hukuncin jarabtata don ya ga ko har zuciya nake baiwa wancan mahaifin hakuri."

- Gwamnan yace.

Sule ya kwatanta marigayi Hassan matsayin mutum mai mutunci wanda a koda yaushe ya ke fatan alheri ga iyalansa.

"Ya girma yana mu'amala mai kyau da dukkan 'yan uwansa. Allah ne kadai yake da karfin ikon kwace shi. Shi kee yanke hukunci kan dukkan kasuwancinmu. A koda yaushe ya na bani shawarar kan abinda ya dace in yi, inda yace ayyukana ba zasu bar ni yin kowanne kasuwanci ba."

Kara karanta wannan

Bayelsa: Karamar Hayaniya ta sa Saurayi Ya Zane Budurwarsa da Suke Zama Tare, Ta mutu

- Yace.

“Allah ya dauke shi ne domin ya gwada juriyata da imani na. Allah bai nemi shawarata ba yayin da zai bani Hassan kuma ba zai nema ba idan zai dauke shi daga gareni."

Bayan wata 7 da aure, 'dan gwamnan Nasarawa ya kwanta dama

A wani labari na daban, Hassan AA Sule, 'dan Gwamnan jihar Nasarawa, ya rasu sakamakon rashin lafiya da yayi fama da ita.

An tattaro cewa, ya rasu a ranar Alhamis bayan watanni bakwai da angwancewa da masoyiyarsa Salamatu Muhammad a wani kayataccen biki da aka yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel