Trump ya tsoma baki a rikicin Rasha da Ukraine, ya yi kukan rasa shugabancin Amurka

Trump ya tsoma baki a rikicin Rasha da Ukraine, ya yi kukan rasa shugabancin Amurka

  • Bayan lokaci mai tsawo bai ce komai ba, rikicin Rasha da Ukraine ta farfado da Donald J. Trump
  • Tsohon shugaban kasar Amurkan ya ce da a lokacinsa ne Vladimir Putin ba zai yi abin da yake yi ba
  • Trump ya na ganin Gwamnatin Joe Biden ta ba Putin da Rasha damar barazanar taba kasar Ukraine

United States – A makon nan tsohon shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya fito yana kuri game da alakarsa da shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin.

Jaridar Independent ta fitar da rahoto a jiya, an ji Donald Trump ya yi magana a kan rikicin Rasha.

A wani jawabin da tsohon shugaban Amurkan ya fitar, ya bayyana cewa tun farko da an yi abin da ya kamata, da ba a shiga wani halin dar-dar a Ukraine ba.

Kara karanta wannan

Solomon Dalung ya nemi a yafe masa na yi wa APC kamfe, ya bi Kwankwaso zuwa TMN

“Da an dauki mataki da kyau, da babu dalilin da zai sa abin da yake faruwa yanzu a kasar Ukraine ya kai ga faruwa.”
“Na san Vladimir Putin sosai, ba zai taba yin abin da yake yi a yanzu a gwamnatin Trump ba, ba za ta taba yiwu ba.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

- Donald Trump

Shugaban Rasha da Trump
Donald Trump da Vladimir Putin Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Joe Biden zai yi magana

Gidan talabijin na Channels TV ta ce kalaman Donald Trump ya zo ne a lokacin da ake sauraron jawabin da shugaban Amurka, Joe Biden zai yi a ranar Laraba.

Da karfe 7:00 na yammacin yau (a agogon Najeriya) Joe Biden zai yi magana a game da matakin da kasar Rasha ta dauka a kan sabaninta da makwabciyarta.

Donald Trump ya caccaki gwamnatin magajinsa watau Biden bayan ta maka takunkumin tattalin arziki. Rahoton ya ce Trump ya na zargin shugaba Biden da rauni.

Kara karanta wannan

Kisan Hanifa: Abin da ya sa Gwamnatin Kano ta ba Abdulmalik Tanko aron Lauya a kotu

Trump ya yabi Putin

Duk da ya yi shiru a kan abubuwan da suke faruwa, CNN ta ce an ji Trump ya na yabon Vladimir Putin a kan matakin da ya dauka na 'yanta wani sashen Ukraine.

A ra’ayin Trump, Putin ya samu abin da yake so domin farashin danyen mai da gas za su tashi.

Amma irinsu Fiona Hill wanda sun yi aiki da Trump, ta shaidawa CNN cewa babu abin da yake gaban tsohon shugaban kasan sai son ransa, ba kishin Amurka ba.

Siyasar Najeriya

Idan mu ka dawo gida za a ji cewa, tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwanso sun kafa sabuwar kungiyar siyasa ta TMN domin karbe mulki a 2023.

Wadanda su ke tare da Sanata Kwankwaso sun hada tsohon minista, Solomon Dalung, Rufai Alkali, Sanata Suleiman Hunkuyi, da Injiniya Buba Galadima.

Asali: Legit.ng

Online view pixel