Bidiyon mace mai tsayin farce inci 12 wanda ta shekara 30 ta na tarawa, ta sanar da yadda ta ke girki

Bidiyon mace mai tsayin farce inci 12 wanda ta shekara 30 ta na tarawa, ta sanar da yadda ta ke girki

  • Wata mata mai suna Cordelia ta tara farce da ya kai inci 12 a jikin ta, ta kwashe tsawon shekaru talatin ta na tara su kuma ta sha alwashin ba za ta sake yanke su ba
  • Matar 'yar asalin Amurka mai shekaru 59 a duniya ta bai wa jama'a a yanar gizo mamaki ganin irin tsayin farcen ta kuma ta ce ta na bai wa jama'a sha'awa
  • Bayan ga yadda ta ke bayanin kan ta da farcen ta, Cordelia ta na kawata da farcen ta masu tsayi da zane kala-kala da kaloli masu kayatarwa

Cordelia mace ce mai shekaru 59 a duniya kuma hanyar bayyana kanta na farko shi ne farcen ta da suka kai tsayin inci 12.

Mazauniyar yankin Virginia din a Amurka ta zama abun kallo a manhajar TikTok ana tsaka da annobar korona yayin da ta wallafa bidiyon ta tana wanke farcen, APost ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tattaki: Yadda bature ya taso daga Landan zuwa Makka da kafa, ya fadi manufarsa

Bidiyon mace mai tsayin farce inci 12 wanda ta shekara 30 ta na tarawa, ta sanar da yadda ta ke girki
Bidiyon mace mai tsayin farce inci 12 wanda ta shekara 30 ta na tarawa, ta sanar da yadda ta ke girki. Hotuna daga Hook On The Look
Asali: Facebook

Ta fara tara farcen a shekarar 1989

A yayin da Hooked on The Look suke tattaunawa da ita, Cordelia ta bayyana cewa ta fara sha'awar tara farce ne bayan da mahaifiyar ta tara wanda ya fi wannan tsayi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Duk da inci 12 ne farcen, matar ta ce a baya ta taba tara farcen da ya kai tsayin inci goma sha shida.

Baya ga sunan da farcen ta suka sa ta yi, Cordelia ta na zane masu kayatarwa a kan farcen. Ta fara tara su tun daga shekarar 1989.

Abinda ta fi so game da farcen

Mutane da yawa suna caccakar ta kan tara farcen kuma sau da yawa mutane a soshiyal midiya kan yi Allah wadai, sai dai ta ce hakan bai dame ta ba.

Cordelia ta ce yadda ake mata magana a kan farcen na daya daga cikin abubuwan da ta fi so kuma yasa ta ke ajiye su.

Kara karanta wannan

Ned Nwoko ya sake sa an cafke Jaruma mai Kayan Mata, alkali ya aike ta gidan yari

Yadda ta ke rayuwa da farcen

A yayin shan alwashin ba za ta taba yanke su ba, matar ta ce ta na amfani da gabar hannayen ta ne wurin yin ayyukan ta na yau da kullum.

Ango ya danƙara wa amarya saki a liyafar bikinsu kan waƙar da ta zaɓa a saka mata

A wani labari na daban, wasu ango da amarya sun kafa sabon tarihi na yin aure mafi gajarta a duniya. Sun rabu ne a yayin da ake liyafar bikin su saboda wakar da amaryar ta zaba.

A take kuwa angon ya dankara wa amaryar saki bayan rikicin da wakar ta janyo yayin da ake tsaka da shagalin bikin a Baghdad.

Kamar yadda aka tattaro, matar ta bukaci a saka mata wata wakar kasar Syria ne mai suna Mesaytara wacce Lamis Kan ya rera.

Asali: Legit.ng

Online view pixel