"Shekarar 9 Muna Soyayya, Kuma Na Fi Shi Albashi": Budurwa Ƴar Shekara 34 Mai Digiri Ta Biya Wa Kanta Sadaki

"Shekarar 9 Muna Soyayya, Kuma Na Fi Shi Albashi": Budurwa Ƴar Shekara 34 Mai Digiri Ta Biya Wa Kanta Sadaki

  • Wata mata ta yi amfani da kudinta ta biya sadakinta a maimakon barin mijinta ya biya; kamar yadda ya ke a al'ada
  • Matar, yar shekara 34 kuma mai digiri guda uku, ta ce ta fi mijin albashi don haka ta ce bari ta taimaka
  • Da farko mijin bai yarda ba amma daga bisani ya amince ya kyalle matar ta biya sadakin

Wata mata wacce ta yi amfani da kudinta ta biya sadaki ta bada labarin yadda lamarin ya faru.

Matar, yar shekara 34 mai suna Zuku wacce ke da digiri guda uku, ta iyayenta sun sha alwashin karbar kudi mai yawa daga mijinta.

Mata ta biya wa kanta sadaki
Budurwa Yar Shekara 34 Mai Digiri Ta Biya Wa Kanta Sadaki, An Ɗaura Aure. Hoto: Photo credit: Klaus Vedfelt and Pollyana Ventura/Getty Images. An yi amfani da hoton ne don misali.
Asali: Getty Images

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da ta ke bawa News24 labarinta, Zuku ta ce ita da kanta ta kawo shawarar biyan sadakinta.

Kara karanta wannan

Aure Daɗi: Bidiyon Yadda Wata Mata Ta Maƙale Wa Mijinta, Ta Hana Shi Rawar Gaban Hantsi

Kalamanta:

"Idan da wani ya taba fada min a shekaru 34, ni ne zan biya wa kai na lobala (sadaki), da na yi dariya. Amma, ya faru - na biya wa kaina lobala, ba zan yi karya ba; ta farko, ina jin kunya."

A al'adun Afirka, nauyin biyan kudin sadaki ya rataya ne kan wuyan miji ba mata ba.

Amma Zuku ta ce ta fi mijinta samun albashi, don haka ya yanke shawarar taimaka masa biyan sadakin.

Mun Yi Soyayya Na Shekara 9, In Ji Zuku

Kafin su yanke shawarar yin aure, Zuku ta ce ita da mijinta sun yi shekaru tara suna soyayya.

Da ta kawo shawarar biya wa kanta sadaki, mijinta bai yarda ba da farko amma daga bisani ya amince da taimakon.

Zuku ta cigaba da bada labarinta:

"Mijina bai goyi bayan hakan ba kuma ya ki amincewa, amma ya bada ma'ana. Yan uwansa za su biya kudin bikin aure kuma za su bawa yan uwa na kyauta.

Kara karanta wannan

Yadda Matashiya Mai Shekaru 34 Ta Biya Sadakin Aurenta Da Kanta

"Kuma na fi shi albashi don haka zan iya biyan kudin labola din. A lokacin, ya ji tamkar shi ba namiji bane amma daga bisan; hakan ya bada ma'ana ga saboda irin rayuwa da za mu gina tare."

Wata Budurwa Yar Najeriya Ta Tunkari Wani Mutum A Bank Ta Tambayi Lambar Wayarsa

Wata budurwa yar Najeriya mai yin bidiyon barkwanci a TikTok ta wallafa wani bidiyo inda ta tunkari wani mutum ta nemi ya bata lambar wayarsa.

Budurwar ta mika masa hannun sun gaisa bayan hakan ta fada masa cewa hannunsa na da laushi kuma ya yi murmushi.

Daga bisani budurwar ta nuna wani takarda da ta ce mutumin ya rubuta mata lambarsa na waya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel