Bidiyon Rolls Royce mai darajar N186m da ake tasi da ita a Dubai ta janyo cece-kuce

Bidiyon Rolls Royce mai darajar N186m da ake tasi da ita a Dubai ta janyo cece-kuce

  • Wani dan Najeriya ya kayatar da mutane a kafafen sada zumunta bayan ya wallafa wani bidiyo da ya dauka a Dubai, daular larabawa
  • Ya wallafa bidiyon wata kasaitacciyar mota sabuwa dal kirar Rolls Royce Phantom wacce ta kai kimar Naira miliyan 186 wacce ake haya da ita
  • A bidiyon an ga yadda mazauna garin suke wucewa ko kallo motar ba ta ishe su ba inda suka dinga wucewa ba tare da nuna damuwarsu ba

Abincin wani gubar wani, abinda ya ke da daraja a nan ba lallai ya samu wani muhimmanci a wani wurin ba.

Tabbas haka maganar ta ke, bayan ganin wani bidiyo wanda wani dan Najeriya ya wallafa a Dubai, daular larabawa daular masu arziki a duniya.

Ya wallafa bidiyonsa cikin wata mota kirar Rolls Royce Phantom wacce tsadar ta ya kai naira miliyan 186 wacce manyan yaran Najeriya su ke karyarta.

Kara karanta wannan

Kudi na magana: Masoya sun tarawa Davido sama da Naira miliyan 120 a ‘yan awanni

Bidiyon Rolls Royce mai darajar N186m da ake tasi da ita a Dubai ta janyo cece-kuce
Bidiyon Rolls Royce mai darajar N186m da ake tasi da ita a Dubai ta janyo cece-kuce. Hoto daga @instablog9ja
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya wallafa yadda ake haya da motar kamar tasi a Najeriya inda mutane suke ta kai komo ba tare da nuna damuwarsu ba. Hasali ma ko kallo motar ba ta ishe su ba.

Darajar motar

Motar ta kai darajar N186 miliyan. Dan Najeriya ya wallafa bidiyon inda ya ke habaici ga manyan yara a Najeriya da ke babatu bayan sun siyasa motar, inda yace a Dubai ba komai bace.

Carbuzz ta bayyana cewa, Rolls Royce Phantom mota ce mai matukar tsada kuma farashin ta ya kai N186 miliyan.

Martanin 'yan Najeriya kan bidiyon

Nan da nan ‘yan Najeriya suka fara tsokaci iri-iri a karkashin wallafar.

Wani icefunds01 ya ce:

“Suna amfani da Rolls Royce Phantom yayin da ake amfani da tasi a Legas don haya da bukukuwa... ba za ka iya biyan kudin hayanta ba ne.”

Kara karanta wannan

Yajin aikin ASUU: FG za ta rabawa jami’o’i biliyan N22.72 a ranar Laraba – Ministan Buhari

Stan_kachinya ce: “A Najeriya ne kadai ake kallon waya kirar IPhone da manyan motoci a matsayin kayan gabas. A can kuwa ba wani abu bane.”

Tenovertenautos ya ce:

“Kada ka gwada jahilcinka a kafar sada zumunta. Ko ba tasi suke amfani da shi ba, hakan ba ya nuna arhar Rolls Royce. Don haka dole a sara wa arziki duk inda aka ganshi.”

Aljannar duniya: Hotunan cikin katafarun gidajen £45m na Ronaldo da motocin alfarma

A wani labari na daban, fitaccen dan wasan kwallon kafa a duniya, Cristiano Ronaldo, mutum ne mai son shakawata da fantamawa a cikin dukiyarsa.

Kamar yadda UK Sun ta wallafa, Ronaldo ya na da gidaje da motoci masu darajar sama da £45 miliyan, daga katafaren gidan na Madeira mai darajar £7 miliyan zuwa motarsa kirar Bugatti mai darajar £8.5 miliyan har kan marsandin sa mai darajar £14,000.

Ronaldo na iya barin gidansa na Cheshire zuwa wadannan gidajen, uku kacal daga cikin katafarun gidajensu masu darajar sama da £23 miliyan.

Kara karanta wannan

N2tr CBN ta rarraba wa masu kananan sana'o'i da kamfanoni a cikin shekara 1, Emefiele

Asali: Legit.ng

Online view pixel