Bayan shekaru 52, an gano mutumin da ya sace N88.1m, an kuma gano inda ya ɓoye kuɗin

Bayan shekaru 52, an gano mutumin da ya sace N88.1m, an kuma gano inda ya ɓoye kuɗin

  • Ba a gano wani mutum, Theodore John Conrad ba, wanda ya sace $215,000 (N88,182,250) daga banki tun 1969 har sai bayan mutuwarsa
  • Bayan wannan gagarumar satar wacce ta ja wa babban bankin asara, ya sauya gari inda ya koma Boston daga Cleveland don ya ci gaba da rayuwa cikin tsanaki
  • Saidai bankin da ya yiwa satar basu farga da yawan kudin da ya sata ba har sai da suka lura bai sake komawa bankin kan aikinsa ba

Kasar Amurka - Theodore John Conrad, wani mutum mai shekaru 20 a watan Yulin 1969, a lokacin ya fara aiki a wani banki da ke Amurka.

Bayan fara aikin ne ya sace $215,000 wanda ya yi daidai da N88,182,250 daga nan babu wanda ya sake ganinsa.

CNN ta ruwaito yadda darajar kudin da ya sata a yanzu ta kai $1.7m (N697,255,000) wanda shi ne mafi girman sata da aka taba yi wa banki a tarihi.

Read also

Da Dumi: Malamin addinin musulunci da CSP na bogi na cikin mutum 14 da aka kama kan kutse gidan Mai Shari'a Odili

Bayan shekaru 52, an gano mutumin da ya sace N88.1m, an kuma gano inda ya ɓoye kuɗin
Conrad ya yi rayuwarsa ba tare da hayaniya ba bayan fashin. Hoto: CNN
Source: UGC

Ya koma wani garin fiye da shekaru 50 da suka shude daga baya ‘yan sanda su ka bayyana cewa ranar Juma’a, 12 ga watan Nuwamba sun gano shi, CTV News ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bayan fashin da ya yi wa bankin, Conrad ya koma wani garin, Boston kuma ya mayar da sunansa Thoman Randele.

Kamar a fim

Wani abu da zai baka mamaki shi ne, gidan mutumin kusa da inda aka shirya fim din nan da ya shahara ‘The Thomas Crown Affair’. A fim din jarumin ya saci $2,000,000 (N820,300,000) daga wani banki.

Dama Conrad ya saci kudin ne a ranar Juma’a bayan an rufe bankin, kuma ba a farga da satar ba sai ranar Litinin da aka lura bai zo aiki ba.

Duk da yadda hotunan mutumin su ka dinga yawo, babu wanda ya samu nasarar jin wani labari akansa.

Read also

Kaico: Jami'in NSCDC ya bindige wani mutum a ƙugunsa yayin da ya ke fitsari a kusa da ofishinsu

Ya ci gaba da rayuwarsa sai a watan Mayun 2021 yana da shekaru 71 ya rasu sakamakon cutar dajin huhu.

Kotu ta ɗaure wani matashi da ya yi asubanci ya tafi coci ya sace kujerun roba

A wani rahoton, wata kotun majistare ta daure wani matashi, Lekan Alaka, mai shekaru 19, watanni 3 bisa satar kujerun roba masu kimar N91,200 daga cocin Mount Zion Angelican.

‘Yan sandan sun kama Alaka da laifin sata kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Alkali Olajumoke Somefun ya yanke hukunci bisa tabbatar da laifin da ya aikata bisa ruwayar Vanguard.

Source: Legit.ng

Online view pixel