Aisha Khalid
4688 articles published since 22 Agu 2019
4688 articles published since 22 Agu 2019
Majalisar koli ta shari’ar musulunci ta Najeriya (SCSN) ta ce ta nada AbdurRashid Hadiyatullah a matsayin sabon shugaban ta. Majalisar ta sanar da ranar Lahadi.
Wani dan Najeriya mai suna Suleiman Seidu ya samu lambar yabon Tusk Conservation kan gudumawar da ya bayar wurin kare rayukan namun dajin da za su iya karewa.
Wasu hazikan maza 'yan asalin Cambodia sun kawo wani sabon salo na hada kayayyaki da kasa inda suka gina gida kacoka da kayan cikinsa da kasa har da kujeru.
Nasir El-Rufai, gwamnan jihar Kaduna, ya ce jami'an tsaro su sakarwa dajika bama-bamai domin ganin bayan 'yan bindiga. Ya ce ko za a yi barna, gara a tada su.
'Yan sanda sun sheke mutum 1 yayin da 'yan daba suka yi yunkurin kone fadar babban basarake Eze Imo. Wasu daga 'yan daban sun sere daji da miyagun raunika.
Bello Turji, gagararren dan bindigan jihar Zamfara, a ranar Litinin ya sako mutane 52 wadanda suka dade a hannunsa, wata majiya ta tabbatar wa da Daily Trust.
Jam'iyyar APC reshen jihar Kaduna ta ce shugabancin ba na mashiririta kuma marasa aikin yi bane face wallafa a kafafen sada zumunta,a martanin ta ga Shehu Sani.
Masari ya ce bai umarci wani ma’aikacinsa ya kama dan jaridar ba kamar yadda darekta janar na labarai ga gwamnan ya sanar ta wata takarda ranar Lahadi da dare.
Alhaji Bashir Tofa, daya daga cikin 'yan takarar zaben shugabancin kasa na 1993, ya rasu kuma an birne shi bayan yi masa jana'iza kamar yadda addini ya tanada.
Aisha Khalid
Samu kari